Ya isheku haka: Masoya Buhari sun gargadi ma su zanga-zanga

Ya isheku haka: Masoya Buhari sun gargadi ma su zanga-zanga

- BCO, kungiyar yakin neman zaben Buhari, ta gargadi matasan da ke zanga-zanga a kan su bar kan titunan da su ka mamaye

- Fusatattun matasa sun cigaba da gudanar da zanga-zanga duk da fitar da sanarwar cewa an amsa bukatarsu, an rushe rundunar SARS

- A cewar BCO, sabon salon da zanga-zangar ke dauka ya tabbatar da cewa balagurbin 'yan siyasa na tunzura ma su zanga-zangar

Kungiyar yakin neman zaben Buhari, BCO, ta yi kira ga ma su zanga-zanga su bar kan titunan da su ka mamaye a jihohin da su ke gudanar da zanga-zangarsu.

Kusan mako guda kenan da matasa su ka fara zanga-zangar neman a rushe rundunar SARS tare da kawo karshen zaluncin jami'an 'yan sanda.

Sai dai, duk da babban sifeton rundunar 'yan sanda ya amsa kiran matasan, ya rushe rundunar SARS, hakan bai kawo karshen zanga-zangar ba.

KARANTA: Kyawawan hotunan matasa 12 da suka hadu a wajen bautar kasa kuma suka yi aure

Abin mamakin ma shine yadda wutar zanga-zangar ke kara ruruwa, mutane da yawa na kara fitowa tare da nuna goyon bayansu.

Sai dai, a cikin wani jawabi da BCO ta fitar ranar Laraba ta bakin shugabanta na kasa, Danladi Pasali, ta ce ma su zanga-zangar na neman wuce makadi da rawa.

Ya isheku haka: Masoya Buhari sun gargadi ma su zanga-zanga
Gwamnan jihar Legas yayin gabatar da jawabi ga masu zanga-zanga a Legas
Asali: Twitter

Jawabin BCO ya bayyana cewa; "mun yi tunanin za su yi aiki da hankali su dakatar da zanga-zangar, amma abin takaici, sun cigaba.

KARANTA: Buhari ya gana da GEJ, Bagudu, Badaru da Buni a Villa (Hotuna)

"Sun cigaba da gudanar da zanga-zanga a wani sabon salo da ke nuna cewa akwai wasu balagurbin 'yan siyasa da ke daukar nauyinsu.

"Cigaba da zanga-zangarsu ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyin 'yan kasa ma su kaunar zaman lafiya.

"Sabon salon da su ka dauka ya nuna cewa tabbas akwai siyasa a boye a cikin cigaba da gudanar da zanga-zangar, a saboda haka su sani: ya ishesu haka, su dakatar da wannan haukan idan har kishin kasa su ke yi."

A karshe kungiyar ta yi kira ga hukumomin tsaro su kawo karshen zanga-zangar tare da tabbatar da dawo da doka da tsari a wuraren da zanga-zangar ta samu karbuwa.

A wani labarin, Wasu da ake kyautata zaton cewa masu garkuwa da mutane ne sun sace matar shugaban masu dauko rahotanni na kungiyar NUJ reshen jihar Cross River, Mazi Judex Okoro.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an sace matar ne da misalin karfe 8 na daren ranar Talata, a yankin Biq Qua, kusa da cocin Apostolic, karamar hukumar Calabar ta tsakiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel