Matar aure ta gurfana gaban kotu bayan ta soka wa makwabciya wuka a kai

Matar aure ta gurfana gaban kotu bayan ta soka wa makwabciya wuka a kai

- 'Yan sandan jihar Osun sun gurfanar da wata dattijuwa mai shekaru 45 a duniya

- Ana zargin matar da soka wa makwabciyarta wuka a kanta bayan sun samu rikici

- Duk da musanta aikata hakan da tayi, an bada belinta tare da dage shari'ar

Rundunar 'yan sandan jihar Osun da ke Osogbo a ranar Alhamis ta gurfanar da wata mata mai shekaru 45 mai suna Olayinka Obaado.

Ana zargi dattijuwar matar da soka wa makwabciyarta mai suna Adekunle Adebayo wuka akanta a Oke-Baale da ke Osogbo.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Razaq Olayiwola, ya sanar da kotun cewa wacce ake zargin ta aikata laifin a ranar 14 ga watan Oktoban 2020 wurin karfe 5:30 na yammaci.

Olayiwola ya sanar da kotun cewa laifin da wacce ake kara ta aikata ya ci karo da sashi na 516 kuma abun hukuntawa a sashi na 355 na dokokin laifuka na jihar Osun.

Wacce ake zargin ta musanta aikata laifin da ake zarginta da shi kuma mai kareta, Okobe Najite ya bukaci a bada belinta.

A hukuncin mai shari'ar, Majistare Adijat Oloyade, ta bada belin matar a kan kudi N50,000 da tsayayye guda daya.

An dage sauraron kara zuwa ranar 26 ga watan Oktoban 2020 domin cigaba.

KU KARANTA: 'Yan sa kai sun kashe mutum 11 da ake zargi da zama 'yan bindiga a Katsina

Matar aure ta gurfana gaban kotu bayan ta soka wa makwabciya wuka a kai
Matar aure ta gurfana gaban kotu bayan ta soka wa makwabciya wuka a kai. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnonin jihohi 19 na arewa sun yi watsi da rushe rundunar SARS

A wani labari na daban, wani mawaki mai suna Amzat Ibrahim, a ranar Alhamis ya sanar da wata kotun gargajiya da ke zama a Ile-Tuntun a Ibadan cewa matarsa fasika ce.

Ya sanar da yadda matarsa mai suna Zainab take lalata da babban amininsa. Amzat ya bayyana wannan zargin ne bayan Zainab ta sanar da kotun cewa yana farautar rayuwarta domin haka take so a raba aurensu.

"Mai shari'a, a gaskiya ni da Zainab muna fada ne saboda halin bin mazanta. Zainab da babban abokina suna fasikanci.

“Ta yi batan dabo na tswon watanni uku inda ta bar gidana. Ta kwashe yarana amma daga bisani sai na gano tana gidan abokina ne kuma aminina," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng