Guntun gatarin ka: Yadda wata mata mai ƴar kucilar mota ta ja hankalin jama'a a yanar gizo

Guntun gatarin ka: Yadda wata mata mai ƴar kucilar mota ta ja hankalin jama'a a yanar gizo

- Wata mata ta je shafin Twitter domin wallafa hotunanta tsaye a gefen sabuwar motarta

- Cikin dan kankanin lokaci wallafar nata ya yi fice inda mabiya shafin Twitter suka dunga bayyana ra’ayinsu kan ƴar kucilar motar

- Yayinda wasu da dama suka dunga dariya game da kankantar motar, wasu sun karfafa mata gwiwar murna da duk wata nasara da ta samu, duk kankantarsa

A rayuwa mutum kan kasance cikin farin ciki a duk lokacin da wani abun alkhairi ya same shi duk kankantarsa. Wata mai amfani da shafin Twitter ta je kafar domin murnar nasarar da ta samu a rayuwarta – inda ta siyi sabuwar mota amma yar kucila.

Da take wallafar a shafinta mai suna TakaTina1, matar ta buga hotonta tsaye a gefen motar mai launin ja inda ta rubuta “Kalli abun Allah.”

Ta wallafa hoton ne domin murnar sabuwar motar da ta siyawa kanta.

Mabiya shafin na Twitter sun je sashin da aka tanada don sharhi domin bayyana ra’ayinsu kan nasarar da matar ta samu.

KU KARANTA KUMA: Da ɗuminsa: Ƴan bindiga sun kashe Liman da mutane 4 a Kogi

Yayinda da dama daga cikinsu ke yi mata ba’a saboda kankantar motar, sauran mutane sun karfafa wa matar gwiwar cewa ta ci gaba da murnar duk wata nasara da ta samu a rayuwa, imma babba ko karami.

Ku karanta wasu daga cikin sharhinsu a kasa:

@TMdunyelwa ya rubuta

“Guntun gatarin ka ya fi sari ka bani.”

@ K_majozi1 ya ce:

“Ba laifi, akalla za ki kai inda za ki.”

@ace_anele ya ce:

“Har wajen rana ne da shi, Allah na gwanin kyauta ne a koda yaushe.”

@MB_Khumalo ya ce:

“Eh, Allah mai girma ne.”

KU KARANTA KUMA: Tashin farashin masara, tumatur, dawa: Babbar jihar Nigeria da ke fuskantar ƙarancin abinci

Guntun gatarin ka: Yadda wata mata mai ƴar kucilar mota ta ja hankalin jama'a a yanar gizo
Guntun gatarin ka: Yadda wata mata mai ƴar kucilar mota ta ja hankalin jama'a a yanar gizo Hoto: @TakaTina1
Asali: Twitter

A wani labari na daban, wata yar Najeriya ta je shafin soshiyal midiya domin murnar nasarar da ta samu bayan ta yi tattaki daga Lagas zuwa Abuja a kan babur.

Matashiyar mai suna Fehintoluwa Okegbenle ta wallafa wasu hotunanta da na sauran mutane da suka yi tafiyar a shafinta na Twitter.

A cewarta, ya dauke su tsawon sa’o’i 13 kafin suka kai Abuja a kan babur.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel