Da ɗuminsa: Ƴan bindiga sun kashe Liman da mutane 4 a Kogi

Da ɗuminsa: Ƴan bindiga sun kashe Liman da mutane 4 a Kogi

- Wasu mahara sun kai farmaki garin Okofi da ke karamar hukumar Kogi ta jihar Kogi

- Yan bindigan sun halaka wani Limamin masallacin Juma'a, Hussaini Mundi da wasu hudu a yayin harin

- Lamarin ya afku ne bayan sallar asubahi a yau Alhamis, 15 ga watan Oktoba

Wasu yan bindiga da ake zaton makasa ne sun kai farmaki garin Okofi da ke karamar hukumar Kogi, jihar Kogi sannan suka harbi wani Limami, Hussaini Mundi, da wasu mutum hudu.

Wani mazaunin garin da aka ambata da suna Zubairu, ya ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 5:56 na safiyar ranar Alhamis, jim kadan bayan kammala sallar asubahi, inda yace yan bindigar sun kai mamaya garin tare da bude wuta ba kakkautawa.

Ya ce marigayin, babban limamin masallacin Juma’ar garin na fitowa daga masallaci bayan sallar asubahi lokacin da yan bindigan suka bude masa wuta, kuma ya mutu ne a nan take.

Da ɗuminsa: Ƴan bindiga sun kashe Liman da mutane 4 a Kogi
Da ɗuminsa: Ƴan bindiga sun kashe Liman da mutane 4 a Kogi Hoto: @linda_ikejii
Asali: UGC

Ya kara da cewa wasu kananan yara mace da namiji wadanda ke hanyar zuwa bahaya a jejin garin suma sun mutu, bayan harbin da yan bindigar ke yi ya same su.

KU KARANTA KUMA: Kalli budurwar da ta tuka babur daga Lagas zuwa Abuja cikin sa’o’i 13 (hotuna)

“Amma abun bakin ciki, wasu magidanta biyu wadanda harbi ya same su, suma sun mutu daga bisani a hanyar kai su asibiti a Lokoja,” in ji shi.

Zubairu, ya ce a take yan bindigar suka tsere bayan aiwatar da harin, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An yi jana’izar babban limamin a fadar Ohimegie na masarautar Igu-Kotonkarfe, Alhaji Abdulrazak Isah Koto a garin Koton-Karfe.

KU KARANTA KUMA: Tashin farashin masara, tumatur, dawa: Babbar jihar Nigeria da ke fuskantar ƙarancin abinci

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan jihar Kogi, DSP Williams Aya, ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Ya ce mutum uku sun rasa ransu a harin sassafe a garin Okofi da ke karamar hukumar Koton-Karfe da ke jihar.

Kakakin yan sandan ya kara da cewa rundunar yan sandan jihar ta fara bincike a cikin lamarin.

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu yan daba dauke da makamai sun tarwatsa zanga-zangar da wasu matasa ke gudanarwa a jihar Kano.

Matasa a jihar dai sun fito domin yin gangami a kan matsalar tsaro da ake fama da ita a arewacin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel