Shugaban kasar Kyrgyzstan Jeenbekov ya yi murabus

Shugaban kasar Kyrgyzstan Jeenbekov ya yi murabus

- Shugaban kasar Kyrgyzstan, Sooronbay Jeenbekov ya sauka daga mukaminsa na jagorancin kasar

- Shugaban ya yi murabus ne biyo bayan zanga-zanga da 'yan kasar suka kwashe kwanaki suna yi na rashin gamsuwa da zaben 'yan majalisu da aka yi

- Shugaban Jeenbekov ya ce baya son tarihi ta rika tuna wa da shi a matsayin shugaban da ya yi sanadin zubda jinin 'yan kasar

Shugban kasar Kyrgyzstan, Sooronbay Jeenbekov ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Alhamis bayan 'yan kasar sun yi kwanaki suna zanga-zanga.

Shugaba kasar ya ce ya sauka daga mukaminsa ne domin kawo karshen rikicin da ya taso sakamakon tsaikon da aka samu yayin zaben 'yan majalisu a kasar a farkon wannan watan.

Shugaban kasar Kyrgyzstan Jeenbekov ya yi murabus
Sooronbay Jeenbekov. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamnan jihar Gombe ya nada dan kabilar Igbo a matsayin hadiminsa (Hotuna)

"Ba zan nace dole sai na cigaba da zama kan mulki ba. Bana son tarihi ta rika tuna wa da ni a matsayin shugaban kasar da ya bari aka zubar da jini aka harbi mutanensa. Na yanke shawarar yin murabu," a cewar Jeenbekov cikin sanarwar da ofishinsa ta fitar.

Tun bayan zaben 'yan majalisa a kasar ta Kyrgyzstan a ranar 4 ga watan Oktoba ake rikici a kasar.

Zanga-zangar ce ta tilasta wa jami'an hukumar zabe na kasar soke sakamakon zabukan sannan aka hambarar da gwamnati kamar yadda BBC ta ruwaito.

Mista Jeenbekov ya zama shugaba na uku a kasar da aka hambarar daga mulki sakamakon zanga-zanga tun shekarar 2005.

KU KARANTA: Zaben kananan hukumomi: Gwamnatin Kano za ta yi wa 'yan takara gwajin kwayoyi

A yayin da ya ke barin ofishinsa, ya yi kira ga 'yan kasar su zauna lafiya inda ya yi gargadin cewa Kyrgyzstan na daf da fada wa cikin rikici.

"Za a tilasta wa sojoji amfani da karfin bindiga don kare kasar. Za a zubar da jini. Ina kira ga bangarori biyun su kwantar da hankulansu," in ji shi.

Ya kuma yi kira ga sabon Farai ministan da aka nada Sadyr Japarov da sauran 'yan siyasan jam'iyyun hamayya su janye magoya bayansu daga babban birnin kasar saboda a samu zaman lafiya a Bishek.

A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a ranar Talata ya amince a ɗauki sabbin malamai 776 don inganta ilimi a makarantun gwamnatin jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne jim kadan bayan gana wa da ya yi da jami'an Ma'aikatar Ilimi na jihar a gidan gwamanti da ke Maiduguri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel