Da albashinsa, dan majalisar tarayya ya gina katafariyar makaranta, ya zuba kayan bukata

Da albashinsa, dan majalisar tarayya ya gina katafariyar makaranta, ya zuba kayan bukata

- Duk da yadda 'yan Najeriya ke sukar shugabanni, akwai masu tausayin talakawa da taimako irin Hon. Armayau Abdulkadir

- Hon. Armayau Abdulkadir dan majalisar dattawa ne mai wakiltar mazabar Dutsin-Ma da Kurfi, wanda yayi abin da mutane da dama ke ta yabawa

- Ya yi amfani da albashinsa tun na farko wurin gina makarantar sakandire mai azuzuwa 12 da duk wani abin amfani na makarantar

Hon Armayau Abdul, dan majalisa ne mai wakiltar mazabar tarayya ta Dutsin-Ma da kurfi da ke jihar Katsina, ya yi amfani da kudinsa wurin gina makarantar sakandare a mazabarsa..

Ya sanya wa makarantar sunan mahaifiyarsa wacce ta rasu ami suna Hajiya Indo, Allah ya gafarta mata.

Ya fara ginin ne da albashinsa na farko a watan Yulin 2019 bayan hawansa kujerarsa.

Makarantar tana da azuzuwa 12, dakin gwaji na kimiyya da fasaha, dakin karatu, ofisoshin malamai, ofisoshin shugaban makaranta da mataimakinsa, da kuma bandakunan malamai da na dalibai.

Hon. Armayau ya inganta azuzuwan makarantar da kujeru na zamani guda 25 a kowanne aji, allo da kuma sauran abubuwan amfani da makarantar zata bukata.

KU KARANTA: Tsaro: FG ta kaddamar sabon shirin tattaunawa da jama'a

Da albashinsa, dan majalisar tarayya ya gina katafariyar makaranta, ya zuba kayan bukata
Da albashinsa, dan majalisar tarayya ya gina katafariyar makaranta, ya zuba kayan bukata. Hoto daga Katsinapost.com.ng
Asali: UGC

KU KARANTA: Ruwa ya yi awon gaba da 'yan mata uku a jihar Jigawa

A wani labari na daban, a makon da ya gabata, gwamnatin jihar Borno ta fara kokarin mayar da 'yan gudun hijira zuwa garuruwan su. Ma'aikatar gyara da mayar da 'yan gudun hijira gidajensu ce take jagorantar shirin.

AFP ta ruwaito yadda mayakan Boko Haram suka shiga gonaki kuma suka farma masu noman rani a kauyen Ngwon, wanda yake da tazarar kilomita 14 ta Arewa zuwa birnin Maiduguri.

'Yan Boko Haram din sun yanka wuyan manoman kuma sun yi musu alama ta masu jihadin Musulunci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel