Cikar Ahmed Musa shekaru 28: Tarihi, albashi, dukiya da aurensa

Cikar Ahmed Musa shekaru 28: Tarihi, albashi, dukiya da aurensa

- A jiya, 14 ga watan Oktoban 2020 ne fitaccen dan kwallo Ahmed Musa ya cika shekaru 28 a duniya

- Fitaccen dan kwallon shine kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya kuma yana aiki da wata kungiya a kasar Saudi Arabia

- Ahmed Musa ya fuskanci kaluable masu yawa, hakan bai sa ya hakura da cimma burikansa ba a rayuwa

Ahmed Musa wanda yake wasa a kungiyar Al-Nassr da ke kasar Saudi Arabia, yana daya daga cikin kwararrun 'yan kwallo a kasar nan. Ya kasance yana taka leda tun yana karamin yaro.

Musa ya fuskanci manyan kalubale a rayuwarsa, amma hakan bai sa ya hakura ba kuma hakan yasa ya cika burinsa na zama babban dan kwallon kafa a duniya.

An haifa Ahmed Musa a ranar 14 ga watan Oktoban 1992, yanzu haka yana da shekaru 28 a duniya. An haifesa a garin Jos da ke jihar Filato.

Sunan mahaifinsa Alhaji Musa. Duk da rasuwar da yayi tun Ahmed yana karamin yaro, har yanzu Ahmed yana tuna mahaifinsa a kusan kowacce tattaunawa da aka yi da shi.

Sunan mahaifiyarsa Sarah Moses kuma 'yar asalin jihar Edo ce. Kirista ce amma ta aura musulmi. Bayan rasuwar maigidanta, ita ta dinga raino tare da tarbiyar yaranta biyar.

Tun bayan gano cewa yana da burin zama dan kwallo, mahaifiyarsa ta cigaba da bashi karfin guiwa har zuwa shahararsa.

Mahaifiyarsa ta rasu a ranar 24 ga watan janairun 2019 bayan fama da tayi da rashin lafiya.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Kungiyoyin arewa sun sanar da ranar fara zanga-zanga maras tsayawa

Cikar Ahmed Musa shekaru 28: Tarihi, albashi, dukiya da aurensa
Cikar Ahmed Musa shekaru 28: Tarihi, albashi, dukiya da aurensa. Hoto daga gettyimages.com
Asali: Getty Images

A bangaren iyali kuwa, Ahmed Musa ya aura mata biyu amma a halin yanzu yana tare da daya ne.

Ya aura Jamila Musa wacce suka haifa 'ya'ya biyu da ita kafin rabuwarsu. A halin yanzu yana auren Juliet Ejue wacce suka haifa yaro daya da ita.

A halin yanzu, yana tare da kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr inda yake karbar albashi duk mako wanda ya kai 60,000 pounds.

Kamar yadda carmart.ng ta wallafa, Musa yana da dukiyar da ta kai N3.8 biliyan.

KU KARANTA: Hotunan ganawar Sarkin Zazzau da Gwamna Nasir El-Rufai a Kaduna

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya kirkiri runduna ta musamman ta makamai da dabaru da za ta maye gurbin runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami.

Sabbin 'yan rundunar da za a fara horar da su a mako mai zuwa za a yi musu gwajin lafiya da kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya yin sabon aikin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel