Kotu ta yankewa barawon molin buga bulo hukuncin daurin shekara guda

Kotu ta yankewa barawon molin buga bulo hukuncin daurin shekara guda

- Kotu ta zartar da hukuncin daurin shekara guda a kan wani magidanci da ya saci molin buga bulo

- Dan sanda mai gabatar da kara ya sanar da kotu cewa wannan shine karo na uku da aka gurfanar da mai laifin

- Mai laifin ya sanar da kotu cewa matarsa na dauke da juna biyu da kuma karamin yaro

Wata kotun majistare da ke zamanta a Osogbo, babban birnin jihar Osun, ta zartar da hukuncin daurin shekara guda a gidan yari a kan wani mutum, Saheed Isola, mai shekaru 40, bayan samunsa da laifin satar molin buga bulo.

An gurfanar da Isola a gaban kotu ranar Laraba bisa tuhuma guda daya; laifin sata.

Dan sanda mai gabatar da kara ya sanar da kotu cewa Isola ya balle shagon wani da kasuwa mai suna Moshood Ishola tare da sace molin buga bulo guda biyu.

Dan sandan mai suna Fagboyinbo ya ce Isola ya saci molin bugo bulo inci 9 da kudinsa ya kai N40,000 da kuma molin buga bulo inci 6 da kudinsa ya kai N30,000. Jimillar kudin molin buga bulon biyu ya tashi N70,000.

KARANTA: Abin da na tattauna da shugaba Buhari a kan zanga-zangar EDNSARS - Gwamnan Legas

A cewar dan sanda, laifin Isola ya sabawa doka kuma an tanadi hukuncin laifin a karkashin sashe na 413 na kundin manyan laifuka na jihar Osun da aka yi wa garambawul a shekarar 2020.

Kotu ta yankewa barawon molin buga bulo hukuncin daurin shekara guda
Kotu ta yankewa barawon molin buga bulo hukuncin daurin shekara guda
Asali: Twitter

ASP Fagboyinbo ya shaidawa kotu cewa Isola ya aikata laifin ne ranar 14 ga watan Oktoba, 2020, da misalin karfe 5:00 na safe a unguwar Lameco.

Isola, wanda ko lauya bai samu ba, ya amsa laifinsa a gaban kotun.

KARANTA: Babbar magana: Buhari zai ruguza EFCC da ICPC, ya bayyana dalili

Da ya ke magana yayin zaman kotun, Isola ya nemi sassauci a hukuncin da za a yanke ma sa saboda matarsa na dauke da tsohon ciki da kuma karamin yaro.

Kazalika, ya sanar da kotun cewa babu wanda ya san an gurfanar da shi a gaban kotu a danginsa kuma ga shi wayarsa bata tare da shi kuma ba zai iya tuna lambar kowa ba.

Sai dai, kafin alkali ya karanta hukuncin kotu, Fagboyingbo ya sanar da kotun cewa; "wannan shine karo na uku da aka taba gurfanar da shi, a karo na farko an ci tararsa N15,000, na biyu kuma an saka shi aiki."

Alkalin kotun, Opeyemi Badmus, bayan ya kammala sauraren duk bayanan da aka gabatar, ya yankewa Isola hukuncin daurin shekara guda a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel