'Yan bindiga sun kai hari birnin Kano, sun ragargaza wurare 3 a rana daya

'Yan bindiga sun kai hari birnin Kano, sun ragargaza wurare 3 a rana daya

- Hankulan mutanen Kano sun tashi a ranar Talata, 13 ga watan Oktoban 2020, inda 'yan fashi da makami suka kai hari wurare uku daban-daban a rana daya

- 'Yan fashin sun iso Kano ne a cikin mota kirar Golf da makamai masu rikitarwa, inda suka kawo hari shagunan dake Takutawa, wani yankin jihar

- Sun isa ne da misalin karfe 8:30 na daren Talata, kamar yadda wani mai gadi dake Dukawuya ya sanar kuma ya ja kunnen jama'a akan harin kafin aukuwar shi

Wani al'amari mai firgitarwa ya faru a ranar Talata, 13 ga watan Oktoba 2020, inda wasu mutane masu makamai suka yi wa 'yan Kano fashi.

Jaridar Sahelian Times ta ruwaito yadda katti 4, majiya karfi suka yi wa mutane fashi a SHY Plaza a Gadon Kaya wuraren karfe 8:30 na dare.

'Yan fashin sun iso Plazar ne a cikin wata mota kirar Golf, kuma sun tsaya a Tukuntawa, wani yankin jihar Kano kusan a jejjere, inda suka rikitar kuma suka yi wa mazauna yankin fashi.

Masu gani da ido sun sanar da HumAngle cewa an ga 'yan fashin a layin Bawo a birnin Kano, inda suka yi wa shaguna da dama fashi.

Kwanakin baya wani mai gadi ya ja kunnen jama'a, inda yace akwai 'yan fashin dake shirin kawo hari anguwar Dukawuya dake Kano, wanda bata da nisa da inda aka yi fashin.

Mutanen da suka waye da yadda 'yan ta'addan ke gudanar da al'amuran su sun sanar da HumAngle cewa 'yan fashi na saka tsoro a zukatan wadanda zasu kaiwa hari kafin su cimma manufarsu, don haka na daya daga cikin dabarun 'yan fashi da masu garkuwa da mutane.

'Yan ta'adda na cigaba da kai hari bankuna, shaguna da kuma wuraren da kudi ke shige da fice Arewacin Najeriya.

KU KARANTA: Ayyuka 774,000: Buhari ya sanar da ranar fara diban ma'aikata

'Yan bindiga sun kai hari birnin Kano, sun ragargaza wurare 3 a rana daya
'Yan bindiga sun kai hari birnin Kano, sun ragargaza wurare 3 a rana daya. Hoto daga HumAngle
Asali: UGC

KU KARANTA: EndSARS: Bidiyon dan sanda yana zazzabga wa tsohuwa mari a wurin zanga-zanga

A wani labari na daban, wani mutum dan Najeriya, shugaban kamfanin tsaro na Fionet, yace , don ya koya wa dansa, Uyiogosa makamar sana'a da kuma zama masa uba nagari, ya daukesa aiki a kamfaninsa.

Yayin da yayi wallafarsa a LinkedIn, ya wallafa hoton dansa sanye da kayan masu gadi.

A yadda ya wallafa, ya jefa wa iyaye tambaya, akan idan zasu iya koyawa yaransu sana'arsu ko kuma zasu barsu hakanan kada su wahala? Felix ya godewa Ubangiji da ya bashi damar taso da yaronsa cikin tarbiyya don su zama 'ya'yan da zasu jagoranci al'umma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel