Zaben kananan hukumomi: Gwamnatin Kano za ta yi wa 'yan takara gwajin kwayoyi

Zaben kananan hukumomi: Gwamnatin Kano za ta yi wa 'yan takara gwajin kwayoyi

- Gwamnatin jihar Kano za ta yi wa dukkan wadanda za suyi takara a zaɓen ƙananan hukumomi gwajin kwayoyi

- Gwamnatin ta ce duk wanda aka samu akwai muggan kwayoyi a jikinsa za a tura shi cibiyar sauya halaye

- Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne don kawar da ta'amulli da miyagun ƙwayoyi a jihar da zai taimaka wurin rage laifuka

Zaben kananan hukumomi: Ganduje ya bada umurnin a yi wa 'yan takara gwajin kwayoyi
Gwamna Abdullahi Ganduje. Hoto daga @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da ɗuminsa: Akeredolu ya gana da Buhari, ya bukaci mataimakinsa ya yi murabus

Gwamnatin jihar Kano da haɗin gwiwar hukumar hana ta'amulli da fataucin miyagun kwayoyi na ƙasa za ta yi wa dukkan ƴan takara a zaɓen ƙananan hukumomi da ke tafe a jihar gwajin kwayoyi.

Za a yi zaɓen ƙananan jihohin na Kano ne a watan Janairun shekarar 2021.

Kwamishinan ƙananan hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo ne ya sanar da hakan yayin bude wani taron wayar da kai na kwana 2 da aka shirya wa ma'aikatan ƙananan hukumomi 44 a jihar don wayar da su game da illolin miyagun ƙwayoyi.

Garo, wanda ya wakilci gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Ganduje wurin taron ya bayyana cewa za a yi irin gwajin ga dukkan ma'aikatan ƙananan hukumomi 44 a jihar.

Ya ce dukkan wadanda aka samu da miyagun ƙwayoyi a jikinsu za a tura su cibiyar sauya halaye.

KU KARANTA: Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35 (Hotuna)

Da ya ke jawabi kan muhimmancin taron, Garo ya ce, "Daga cikin dalilan da yasa muka bada umurnin yin wannan taron bitan shine domin wayar da kan ma'aikatan mu a ƙananan hukumomi 44 game da illolin shan miyagun kwayoyi, hakan yasa mai girma Gwamna ya bada umurnin yin gwajin a kan dukkan ma'aikatan ƙananan hukumomi 44 don tabbatar da ba mu ta'amulli da miyagun ƙwayoyi.

Ya ce an zaɓo mahalarta taron daga ƙananan hukumomi 44 da ke jihar ne don su isar da saƙon ga matasa da sauran al'umma a yankunan su.

"Nan ba da daɗewa ba mai girma gwamna zai bada umurnin yi wa dukkan ma'aikatan ƙananan hukumomi 44 gwaji. Kun san cewa zaɓen ƙananan hukumomi na tafe; mai girma gwamna ya bada umurnin duk wanda zai yi takarar kansila ko shugaban ƙaramar hukuma sai ya tafi hedkwatar NDLEA da ke Kano an masa gwaji.

"Kwamandan NDLEA, Dakta Ibrahim Abdul ya jinjinawa ƙoƙarin da gwamnatin ke yi na hana ta'amulli da miyagun ƙwayoyi da ya ce zai taimaka rage laifuka a jihar," ya kara da cewa.

A wani labarain, Shugaba Buhari ya assasa tubalin ginin jami'ar musulunci ta As-Salam Global University, Hadejia, mallakar kungiyar Jama'atu Izalatul Bidi'ah Wa'iqamatis Sunnah, JIBWIS, jihar Jigawa.

Shugaban ƙasar da ministan sadarwa , Dakta Isa Pantami ya wakilta ya assasa tubalin ginin jami'ar a wurin taron.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel