Abubuwa 5 da ya kamata mutum ya guji aikatawa a yayin zanga-zanga

Abubuwa 5 da ya kamata mutum ya guji aikatawa a yayin zanga-zanga

- Matasa a fadin kasar na ci gaba da gudanar da zanga-zangar neman a soke rundunar SARS

- Masu zanga-zagar sun gabatar da bukatun da suke so gwamnati ta biya masu

- Mun zakulo maku wasu abubuwan da bai kamata ace mai zanga-zanga ya aikata ba

A yan kwanakin nan da ake ciki, ana ta gudanar da zanga-zangar a birane da manyan garuruwa da dama a kasar domin neman a kawo karshen cin zarafin da ake zargin yan sanda da aikatawa al’umma.

Gwamnatocin tarayya da na jiha sun yarda cewa hakkin yan kasa ne gudanar da zanga-zangar lumana.

Abubuwa 5 da ya kamata mutum ya guji aikatawa a yayin zanga-zanga
Abubuwa 5 da ya kamata mutum ya guji aikatawa a yayin zanga-zanga Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Twitter

Ga abubuwan da bai kamata ka yi ba idan kana cikin masu zanga-zangar kawo karshen SARS da ke gudana.

KU KARANTA KUMA: EndSARS: Gwamnan Lagas ya gana da Buhari a Aso Rock

1. A guji rikici:

Ba dole sai zanga-zanga ya zama tashin hankali ba. Su kasance an gabatar da muradan yinsu cikin lumana. Dole ka guji abunda zai sa ya zama rikici, koda kuwa an tunzura ka ne.

2. Ban da cin zarafi:

Babu amfanin cin zarafin jami’an tsaro, mazauna yankin da ake zanga-zanga da kuma masu wucewa. Ya wadatar ku bayyana kokenku har sai an dauki matakan da suka dace.

3. Ban da sata:

Satar kayayyakin gwamnati da na mutane masu zaman kansu zai gurbata halascin zanga-zangar.

4. Ban da watsar da shara:

Ka da a watsar da shara a tituwa. A zubar dasu a wajen da ya kamata. Abunda ake zanga-zanga a kai ya kasance abun damuwa. Ba a gyara kuskure da kuskure.

Idan kuka gama da kwalayen sanarwarku da sauransu ku yadda su a inda ya kamata. Ku tsaftace Najeriya.

KU KARANTA KUMA: 2023: An bayyana sunayen yan takara 10 da ka iya maye gurbin Buhari daga kudu maso gabas

5. Ban da cutar da kowa:

Akwai rahotannin cutar da mata. Hakan bai dace ba. Ba zai yiwu mu haifar da wani barna ba yayin yakar wani.

A wani labarin, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya kirkiri runduna ta musamman ta makamai da dabaru da za ta maye gurbin runduna ta musamman ta yaki da fashi da makami.

Sabbin 'yan rundunar da za a fara horar da su a mako mai zuwa za a yi musu gwajin lafiya da kwakwalwa domin tabbatar da cewa za su iya yin sabon aikin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel