EndSARS: Rundunar 'yan sandan Lagos ta kwace makamai daga hannun jami'an SARS

EndSARS: Rundunar 'yan sandan Lagos ta kwace makamai daga hannun jami'an SARS

- Rundunar 'yan sandan jihar Lagos ta ce ta kwace makaman da ke hannun jami'an sashen dakile fashi da makami FSARS na jihar

- Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Hakeem Odumosu ya bayyana hakan, yana mai cewa, yanzu an rushe sashen jami'an, ba sa kara yin aiki

- Haka zalika, ya karyata rahotannin cewa an kashe wami mai zanga zanga a Surulere a ranar Litinin, yana nuni da cewa, dan kallo ne aka kashe

Kwamishinan 'yan sandan jihar Lagos, Hakeem Odumosu, ya ce bin umurnin Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda, Mohammed Adamu, na ruguza sashen rundunar SARS.

Odumosu, wanda ya gana da wasu lauyoyi da suke zanga zanga kan cin zarafin da jami'an SARS ke yiwa jama'a, ya ce tuni aka kwace makamai daga hannun jami'an rundunar SARS.

Ya kara da cewa masu laifuka da ke ajiye a karkashin SARS an mayar da su karkashin sashen binciken laifukan ta'addanci a Panti, domin ci gaba da bincike.

KARANTA WANNAN: Yan sanda sun kashe masu zanga zangar EndSARS guda 10 - Amnesty

EndSARS: Rundunar 'yan sandan Lagos ta kwace makamai daga hannun jami'an SARS
EndSARS: Rundunar 'yan sandan Lagos ta kwace makamai daga hannun jami'an SARS - @guardian
Asali: Twitter

Ya bai wa lauyoyin da ke zanga zangar tabbacin cewa ba za su sake ganin wani jami'in SARS a cikin ayyukan rundunar 'yan sandan ba.

Kwamishinan ya ce, "Duk wani umurni daga Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda mun bi shi. Za ku gani a nan Lagos, muna da sashe sashe, wadanda ba sa daukar makamai ko zaluntar jama'a.

"Amma tun daga ranar da Sifeta Janar ya ruguza sashen SARS mu ma muka ruguza su a nan, mun karbi makamansu, yanzu sun koma sanya kakin 'yan sanda ba na sashen su ba."

KARANTA WANNAN: An tsige kakakin majalisar jihar Edo, Francis Okiye

Odumosu, wanda ya jinjinawa masu zanga zangar bisa jagorancin lauyan kare hakkin bil Adama, Inibehe Effiong, na nuna dattako, ya kuma ce babu mutum daya da aka kashe a zanga zangar jihar.

Ya ce mutumin da ya mutu sakamakon harbin bindiga a Surulere a ranar Litinin, ba ya daga cikin masu zanga zangar, amma matuki ne, wanda ya zo kallon abunda ke faruwa a titin.

A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasar Nigeria, Atiku Abubakar, a ranar Lahadi ya jinjinawa matasan Nigeria bisa jajurcewarsu na yakar zaluncin da rundunar 'yan sanda ke yi.

Atiku, ya nuna gamsuwarsa, kan yadda matasan kasar suka hurawa rundunar 'yan sanda wuta har sai da ta rushe sashen rundunar na FSARS da ke yaki da fashi da makami.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel