Da duminsa: Sojoji sun lallasa masu zanga-zanga a Abuja, sun fasa kan dan jarida (Bidiyo)

Da duminsa: Sojoji sun lallasa masu zanga-zanga a Abuja, sun fasa kan dan jarida (Bidiyo)

- Bayan watsawa masu zanga-zanga ruwan zafi da yan sanda sukayi, Sojoji suna dukansu a Abuja

- Matasan sun kai zanga-zangarsu majalisar dokokin tarayya

- Sojojin sun kwace kayan aikin gidan jarida tare da dukan yan jarida

Sojojin da ke gaban kofar shiga majalisar dokokin tarayya a ranar Talata sun fasa kan dan jaridan Arise TV dake daukan hotunan yadda zanga-zangan #ENDSARS ke gudana a birnin tarayya.

A cewar wakilin Arise TV, Ferdinand Duruoha, wannan shine karo na biyu da jami'an tsaro ke cin mutuncinsu.

Sojojin sun tare hanya ne domin hana masu zanga-zanga isa kofar shiga majalisar dokokin.

Duk da yadda masu zanga-zangan ke gudanar da abubuwan cikin lumana, sojojin suka lallasa yan jarida da wasu matasan dake zanga-zanga kuma suka kwacewa jaridar Arise kamarori.

Sojojin sun doki dan jaridan ne yayinda yake daukan bidiyon abinda ke faruwa kai tsaye.

Duk da haka, dan jaridar, Duruoha, bai daina magana ba.

"Oga ka kwace kamaran Arise TV. Mutane na kwance a kasa kuma kana dukansu da gindin bindigarka," Yace

KU KARANTA: Ba zamu yarda ba, sai ka janye - Sanatocin PDP kan nadin hadimar Buhari matsayin kwamishana a INEC

Da duminsa: Sojoji sun lallasa masu zanga-zanga a Abuja, sun fasa kan dan jarida (Bidiyo)
Kofar shiga majalisa
Asali: Original

DUBA NAN: Bayan watanni 3 da dakatad da shi, gwamnan jihar Bauchi ya mayar da Sarkin Misau kan kujerarsa

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel