Bai kamata a saurari ma su zanga-zangar ENDSARS ba - Bidiyon Jarumi Zaharaddeen Sani

Bai kamata a saurari ma su zanga-zangar ENDSARS ba - Bidiyon Jarumi Zaharaddeen Sani

- Jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), Zaharaddeen Sani, ya bayyana ra'ayinsa a kan zanga-zangar ENDSARS

- Zangar-zangar neman a soke rundunr SARS ba ta samu karbuwa ba a jihohin arewa maso yamma da arewa maso gabas

- Wasu matasa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS

Zaharadden Sani, Jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), ya ce a tunaninsa kuskure ne jama'a su ke gudanar da zanga-zanga a kan jami'an 'yan sanda ba 'yan bindiga da ke kashe mutane ba

A cikin wani faifan bidiyo da Legit.ng Hausa ta ci karo da shi a dandalin sada zumunta, an jiyo Jarumin ya na bayyana cewa; "sai jami'an 'yan sanda za a yi wa zanga-zanga, me ya sa jama'a ba za su yi wa gwamnati zanga-zanga ba saboda 'yan ta'adda sai saboda dan SARS guda daya,?

"Ko su 'yan bindiga tsoronsu ake ji? su na kashe mutane ba iyaka, amma ba za a iya fitowa a yi zanga-zanga saboda hakan ba, sai saboda laifin dan SARS guda daya.

DUBA WANNAN: Yan sanda sun kashe masu zanga zangar EndSARS guda 10 - Amnesty

"Ni a ganina hakan kuskure ne, bai kamata shugaban rundunar 'yan sanda ya sauraresu ba, ya fada mu su cewa aiki ya yi ma sa yawa, akwai aiyuka a gabansa da yawa, saboda 'yan bindiga su na ta kashe mutane," kamar yadda Jarumin ya bayyana.

Bai kamata a saurari ma su zanga-zangar ENDSARS ba - Bidiyon Jarumi Zaharaddeen Sani
Wasu ma su zanga-zangar ENDSARS
Asali: UGC

A ranar Litinin ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa a wani faifan bidiyo da jaridar The Cable ta wallafa an ga wasu ma su zanga-zanga sun hada kai tare da ceton wani dan sanda da wasu 'yan daba ke nufin cutarwa.

DUBA WANNAN: Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe basarake Alhaji Musa Abubakar a gidansa

Duk da babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP) ya sanar da cewa an rushe rundunar SARS, har yanzu fusatattun matasa ba su daina fitowa domin gudanar da zanga-zanga ba.

A yayin da matasan ke cigaba da gudanar da zanga-zangar, wasu matasa a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayan rundunar SARS a ranar Talata.

Matasan sun bukaci a dawo da SARS sannan a tura jami'an rundunar zuwa jihar Borno domin su yaki 'yan Boko Haram.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel