Bayan kwana 2 da 'yan bindiga suka kai hari Kaduna, shugabannin tsaro sun kai ziyara

Bayan kwana 2 da 'yan bindiga suka kai hari Kaduna, shugabannin tsaro sun kai ziyara

- Kwamishinan ma'aikatar tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya raka wasu manyan jami'an tsaro Kidandan

- Sun kai ziyarar ne sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai wa kauyen har suka kashe mutane 9 kuma suka kona gidaje da babura

- Aruwan yayi wa mutanen Kidandan ta'aziyya, kuma yace ya wakilci Gwamna El-Rufai, tare da tabbatar musu da ci gaba da basu tsaro yadda yakamata

Kwamishinan ma'aikatar tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya raka wasu manyan jami'an tsaro zuwa wasu unguwanni 2 da 'yan bindiga suka kai hari a ranar Litinin.

Wuraren da 'yan ta'addan suka kai hari sun hada da Kadai da Kidandan dake karamar hukumar Giwa a jihar.

Jaridar Premium times ta ruwaito yadda 'yan bindigan suka kashe mutane 9 a kauyen Kadai, kuma suka kona wasu gidaje da babura, wanda hakan yaja 'yan kauyen sukayi ta guduwa daga gidajensu.

Kamar yadda mazauna garin suka tabbatar, an birne wadanda 'yan bindigan suka kashe a Kidandan ranar Lahadi, da misalin karfe 2 na rana kamar yadda Musulunci ya tanadar.

Wani mazaunin garin yace, sun kwashe mata da kananan yara daga Kauyukan.

Kamar yadda yace, "Mun umarci matanmu da yaranmu da su bar unguwannin mu, su koma makwabtan mu saboda tsaro."

Mazaunan garin sunce, a ranar Lahadi jami'an tsaro suka yi ta bata-kashi da 'yan bindiga, har suka kashe 'yan bindigan da dama.

Dagacin Fatika, Nuhu Umar, ya sanar da Aruwan da kuma manyan jami'an tsaron yadda al'amarin ya faru a ranar Litinin.

Aruwan yace, ya wakilci gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai don nuna wa 'yan kauyen alhininsu, da tabbata musu da cewa suna tare da su, kuma za su yi iya kokarinsu wurin bada tsaro da kula da rayukansu.

KU KARANTA: Sadio Mane: Hotuna da bidiyon motocin da ya mallaka da kuma darajarsu

Bayan kwana 2 da 'yan bindiga suka kai hari Kaduna, shugabannin tsaro sun kai ziyara
Bayan kwana 2 da 'yan bindiga suka kai hari Kaduna, shugabannin tsaro sun kai ziyara. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Masu zanga-zanga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun harbi 'yan sanda 3

A wani labari na daban, an tabbatar da mutuwar mutane 12 sannan mutane 7 sun samu munanan raunuka a wani kauye a jihar Kaduna ranar 11 ga watan Oktoban 2020.

Bayan harin da 'yan bindiga suka kaiwa kauyukan Kidandan da Kadai dake karamar hukumar Giwa dake jihar Kaduna ne aka tabbatar da mutuwar mutane 12 da mutane 7 da suka ji munanan raunuka.

Kamar yadda wadanda suka tsallake rijiya da baya suka tabbatar, wasu 'yan ta'adda da ke tafe da miyagun makamai, sun kaiwa kauyen Kidandan hari a ranar Juma'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel