Da duminsa: Masu zanga-zanga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun harbi 'yan sanda 3

Da duminsa: Masu zanga-zanga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun harbi 'yan sanda 3

- Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas ya sanar da cewa an harba jami'ansu uku a ranar Litinin

- Muyiwa Adejobi ya tabbatar da cewa masu zanga-zanga suna kai musu hari har ofishinsu a jihar Legas

- Masu zanga-zangar dai sun hada da matasa masu bukatar a kawo karshen cin zarafin da 'yan sanda ke yi wa jama'a

Rundunar 'yan sandan jihar legas ta ce masu zanga-zanga sun harba jami'anta uku a ranar Litinin.

Jaridar The Cable ta wallafa yadda masu zanga-zanga suka rufe titunan Lekki, Surulere da Ikeja a jihar Legas inda suke bukatar a gyara tsarin ayyukan 'yan sanda.

Bayan zanga-zangar matasa a dukkan fadin kasar nan, Mohammed Adamu, Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya ya sanar da rushe rundunar 'yan sanda ta musamman ta yaki da fashi da makami.

Amma kuma har yanzu matasa masu zanga-zangar sun ki barin titunan.

A yau ne jaridar The Nation ta bayyana cewa matasa sun kai wa ofishin 'yan sanda a jihar Legas hari.

A kalla masu zanga-zanga biyu 'yan sanda suka harba a yankin Surulere da ke jihar legas a ranar Litinin.

An gano cewa hakan ya faru ne bayan da 'yan sanda suka bude wa masu zanga-zangar ruwan wuta.

A wata tataunawar waya da aka yi da kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Muyiwa Adejobi, ya ce an harba 'yan sanda uku a ranar Litinin.

Adejobi ya ce bashi da labarin mutuwar ko daya daga cikin masu zanga-zangar, amma ya kara da cewa sun kai hari ofishin 'yan sandan.

KU KARANTA: Ministan Buhari da babban basarake sun sha da kyar hannun 'yan daba

Da duminsa: Masu zanga-zanga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun harbi 'yan sanda 3
Da duminsa: Masu zanga-zanga sun kai hari ofishin 'yan sanda, sun harbi 'yan sanda 3. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan Akeredolu da mataimakinsa suna murnar nasarar da suka samu

A wani labari na daban, hukumar 'yan sandan Najeriya a ranar Lahadi, 11 ga watan oktoban 2020, ta ji koken jama'a inda sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya soke runduna ta musamman da ke yaki da fashi da makami (SARS).

Rusa rundunar wacce shugaban 'yan sandan Najeriya ya sanar a jawabin da yayi ga 'yan kasa, babu shakka ya kafa tarihi.

Hakan ya biyo bayan gagarumin zanga-zanga da matasan Najeriya suka dinga yi tun daga ranar Alhamis da ta gabata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel