Ku yi rayuwa mai kyau, ko za ku samu makoma kyau - Obasanjo ya shawarci 'yan Najeriya

Ku yi rayuwa mai kyau, ko za ku samu makoma kyau - Obasanjo ya shawarci 'yan Najeriya

- Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya aike da sako mai muhimmaci ga 'yan Najeriya

- Ya yi kira ga jama'a da su yi aiki nagari domin samun shiga aljanna idan an mutu

- Ya sanar da hakan a taron godiya ga Ubangji bayan birne matar tsohon dan majalisa da aka yi

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bukaci 'yan Najeriya da su yi rayuwa tagari saboda su samu damar shiga aljanna.

Obasanjo ya sanar da hakan ne a wani taron hadin kai da aka yi na wata Majami'a da ke Ogba a jihar Legas.

An yi taron ne domin mika godiya ga Ubangiji a kan nasarar da aka samu wurin birne Olufunsho Salako, matar tsohon dan majalisar wakilai, Apostle Dave Salako.

Olufunsho ta rasu a ranar Lahadi, 9 ga watan Disamban 2020 tana da shekaru 59 a duniya sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

A wasikar ta'aziyya da Obasanjo ya aike wa Dave, wanda ya wakilci mazabar Remo ta tarayya tsakanin 2003 da 2011, ya ce mutuwa tabbacin rashin tabbas na rayuwa ne.

Tsohon shugaban kasar ya bukaci jama'a da su ji tsoron Ubangiji.

Yayin taron mika godiyar ga Ubangiji, Obasanjo wanda ya gudanar da huduba, ya samu wakilcin dansa mai suna Seun.

Obasanjo ya ce aljanna tabbaci ce ga marigayiya Olufunsho saboda daga shaidar jama'a, tana son kowa kuma ta matukar kula da iyalanta.

"A duk lokacin da Kirista ya rasu, ya kwanta bacci ne. A ranar karshe, duk za su tashi kuma a yi musu hisabi. Babu shakka za a yi wa dukkan Kiristoci hisabi," ya kara da cewa.

KU KARANTA: Bidiyon ragargazar da dakarun soji suka yi wa 'yan bindiga a Katsina

Ku yi rayuwa mai kyau, ko za ku samu makoma kyau - Obasanjo ya shawarci 'yan Najeriya
Ku yi rayuwa mai kyau, ko za ku samu makoma kyau - Obasanjo ya shawarci 'yan Najeriya. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke mace mai ciki wata 9 da wasu matasa 2 a kan fashi da makami

A wani labari, jama'a da yawa kan zauna su zuba ido ko kuma su nemi wurin boyewa matukar ana aikata laifi saboda tsoron kada ya shafesu.

Duk da bai wa kai kariya ba abu ne mara kyau ba, kawai yana nuna yadda jama'a ke mutunta rayuwarsu ne da gudun ta subuce musu.

Amma kuma, akwai jama'a da suka kasance jarumai wadanda saboda kokarinsu basu iya zuba ido su ga ana cutar da wasu.

Wani bidiyo mai matukar firgitarwa ya fada kafafen sada zumuntar zamani inda 'yan daba ke kokarin garkuwa da wata yarinya da rana tsaka yayin da take cin abinci da mahaifiyarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel