Kundin kasafin kudin da Shugaban kasa ya gabatar ya saba dokar kasa inji Atiku

Kundin kasafin kudin da Shugaban kasa ya gabatar ya saba dokar kasa inji Atiku

- Atiku Abubakar ya soki yadda aka tsara kasafin kudin shekarar 2021

- ‘Dan siyasar ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sake lissafi

- Atiku ya ce bashin da ake shirin karbowa a badi, ya zarce 3% na GDP

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya kushe kasafin kudin shekara mai zuwa da shugaban kasa ya gabatar a gaban majalisar tarayya.

Alhaji Atiku Abubakar ya ke cewa wasu daga cikin abubuwan da gwamnatin tarayya ta kawo a a kundin kasafin kudin na 2021, sun ci karo da dokokin kasa.

Jagoran adawar kasar ya bukaci shugaban kasar Najeriya da mukarrabansa, su je su sake zama a kan kundin kasafin na badi, da nufin ceto tattalin arzikin kasa.

KU KARANTA: Kasafin kudi: Gwamnati ba za ta rage farashin man fetur da wuta ba

A jiya ranar Juma’a ne Abubakar ya fitar da wani dogon jawabi da ya yi wa take da: “The 2021 Budget Proposal Contravenes The Fiscal Responsibility Act.”

‘Dan takarar shugaban kasan na PDP a 2019 ya yi kira ga shugaban kasa ya yi wa kundin gyare-gyare, ta yadda kasafin ba zai ci karo da dokar batar da kudi ba.

Haka zalika, Atiku Abubakar ya bukaci ayi wa kasafin kudin kasar kwaskwarima ta yadda za a iya shawo kan matsalar tattalin da ke damun Najeriya a halin yanzu.

“Kasafin ya na da gibin Naira tiriliyan 5.21. Wannan kaso ya kai kusan 3.5% na jimillar tattalin arzikin Najeriya a 2019, hakan ya saba da dokar kudi ta 2007.”

KU KARANTA: Duk wanda bai cikin IPPIS, bai da albashi - Buhari

Kundin kasafin kudin da Shugaban kasa ya gabatar ya saba dokar kasa inji Atiku
Atiku tare da Shugaban kasa Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Atiku ya kara da cewa sashe na 12 na wannan doka ya ce bai halatta a samu gibin fiye da 3% na karfin GDP a kasafin kudin da za a gabatar a gaban majalisa ba.

Ya ce: “Najeriya ta na GDP na $447b a 2019. 3% na wannan shi ne $13.3, idan aka yi lissafin Dala a kan N379, wannan adadi zai ba ka Naira Tiriliyan 5.07”

Don haka ne Atiku ya ce gibin da za a samu a kasafin 2021 ya zarce abin da doka ta yi tanadi.

A makon jiya, mun kawo maku dalla-dallar yadda Najeriya za ta batar da kudin kasafin shekara mai zuwa, inda ake sa ran a batar da Naira tiriliyan 13.08.

Gwamnatin Najeriya ta ci babban buri na kashe makudan kudin da ba ta taba batarwa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel