Kiran dan majalisa dan luwadi, jahili a Facebook: Kotu ta tsare matashi a Gombe

Kiran dan majalisa dan luwadi, jahili a Facebook: Kotu ta tsare matashi a Gombe

- Kotu ta bada umurnin ajiye wani matashi a Gombe a gidan gyaran hali saboda zarginsa da zagin dan majalisar jihar a Facebook

- Dan majalisar mai wakiltan Kumo ta Yamma, Abdullahi Abubakar ya ce matashin ya wallafa rubutu inda ya kura shi dan luwadi, jahili kuma makaryaci

- Wanda ake zargin ya musanta aikata laifin kuma kotu ta bada belinsa amma ya gaza cika ka'idojin belin

Kotun Majistare a jihar Gombe ta tsare wani Khalid Abdallah mai shekaru, 25, a gidan gyaran hali saboda zagin wani dan majalisar jihar a dandalin sada zumunta ta Facebook.

Wanda ake zargin mazaunin Kashere a karamar hukumar Akko a jihar Gombe ya yi amfani da shafinsa na Facebbok ya rubuta kalaman batanci da dan majalisa mai wakiltan Akko ta Yamma a majalisar jihar, Abdullahi Abubakar.

Kiran dan majalisa dan luwadi a Facebook: Kotu ta tsare matashi a Gombe
Abdullahi Abubakar. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dan haya ya kashe mai gidan haya saboda ya hana shi kawo mata gida

Kamar yadda rahoton da 'yan sanda suka karanto wa wanda ake zargin a lokacin da ya gurfana a kotu ta nuna, a ranakun 10, 11, 14 da 19 na watan Satumba wanda ake zargin ya wallafa a shafinsa cewa dan majalisar dan luwadi ne, jahili kuma makaryaci.

"Cewa kai Khalid Abdullahi, 25, na garin Kashere a karamar hukumar Akko a ranar 10, 11, 14, da 19 na watan Satumba ka yi amfani da shafinka na Facebook ka zagi dan majalisa mai wakiltan Kumo ta Yamma, inda ka rubuta cewa shi dan luwadi ne, jahili kuma makaryaci, an kuma hada da hoton wanda ya shigar da karar," kamar yadda aka karanto a kotun.

Dan sanda mai shigar da kara, Habibu Danjuma Juwara ya sanar da kotun cewa wannan rubutun karya ne kuma da gangan aka yi don cin mutuncin wanda ya yi karar duk da cewa wanda ya hallafa ya san rubutun zai bata wa dan majalisar suna.

KU KARANTA: Dattijo mai shekaru 106 ya auri sahibarsa mai shekaru 35 (Hotuna)

Mai shigar da karar ya ce hakan ya saba wa sashi na 393 da 399 na dokar Penal Code.

Wanda ake zargin ya musanta zargin ya kuma nemi beli ta hannun lauyansa Barrister Saidu Muazu Kumo.

Juwara ya ki amince da bada belin inda ya ce wanda ake zargin zai iya kawo cikas ga binciken.

Alkalin kotu Japhet Maida ya bada belin wanda ake zargin amma sai ya kawo mutum biyu da za u tsaya masa ciki har da Hakimin Kashere.

Wanda ake zargin ya gaza cika ka'idojin belin hakan yasa kotu ta bada umurnin a ajiye shi a gidan gyaran hali. An daga cigaba da shari'ar zuwa ranar Laraba 14 ga watan Oktoba.

A wani labarin, Jam'iyyar PDP ta ce bata amince da nada shugaban jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, Farfesa Etiyope Ogunbodede a matsayin baturen zabe na zaben gwamna da za ayi ranar Asabar a jihar Ondo ba.

Shugaban kwamitin yakin neman zabe na kasa na PDP, wanda shine gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ne ya sanar da hakan yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Alhamis a Akure.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel