Dan zazzabga mata mari nayi - Sanata Abbo ya daukaka kara a kan tarar N50m

Dan zazzabga mata mari nayi - Sanata Abbo ya daukaka kara a kan tarar N50m

- Sanata Elisha Abbo, ya kalubalanci hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke masa

- Kamar yadda kotun ta bayyana, an kama sanatan da laifin cin zarafin wata mata mai tsaron shago a Abuja

- Amma kuma Sanatan ya ce 'dan cin zarafinta' yayi ba wai take mata wani hakki na dan Adam ba

Elisha Abbo, Sanata mai wakiltar mazabar Adamawa ta arewa, ya daukaka kara inda yake kalubalantar hukuncin wata babbar kotun tarayya wacce ta ci tararsa naira miliyan 50 a kan cin zarafin wata mata.

A 2019, 'yan sanda sun gurfanar da Abbo a gaban wata kotun majistare da ke Zuba, a kan zarginsa da laifin cin zarafin wata mata mai suna Osimibibra Warmate a wani shago a Abuja.

Duk da bidiyon shaidar al'amarin, Abdullahi Ilelah, alkalin kotun ya ce babu wani tuhuma da sanatan zai amsa inda ya kori karar.

Amma kuma, Warmate ta mika wata karar ta daban a wata babbar kotu tarayya da ke ABuja kuma a ranar 28 ga watan Satumba, Mai shari'a Samira Bature ta yanke wa Sanatan hukuncin biyan Warmate miliyan 50.

A daukaka karar da sanatan yayi, ya dogara da abubuwa uku inda yace zarginsa ake da "dan cin zarafi" kuma ba azabtar da mutuma ba, don haka zarginsa da ake da take hakkin dan Adam bai dace ba.

Sanatan ya kara da cewa, tarar naira miliyan 50 da aka bukaci ya biya wacce ya dan ci zarafin ta yi yawa.

KU KARANTA: Allah ya yi wa DG na kungiyar dattawan arewa rasuwa

Dan zazzabga mata mari nayi - Sanata Abbo ya daukaka kara a kan tarar N50m
Dan zazzabga mata mari nayi - Sanata Abbo ya daukaka kara a kan tarar N50m. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Makarfi ya yi martani a kan nadin Sarki Ahmed Bamalli Zazzau

A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Talata, 6 ga watan Oktoba ya ce Najeriya tana da miliyoyin mutane da ke fama da matsanancin talauci.

Ya fadi hakan yayin da yake jawabi a wani taro a fadar shugaban kasa Abuja. Ya ce shugabannin da aka zaba basu da amfani indai har basu hada karfi da karfe wurin taimako a kan matsalar nan ba.

Ya ce, "Dole ne kowanne shugaba ya fahimci yadda zai tafiyar da mulkinsa. Idan aka kalli halin da miliyoyin talakawan Najeriya suke ciki, gashi yanzu cutar COVID-19 ta kara dagula komai, talauci da rashin aikin yi sun yawaita."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel