Tattalin arzikin Najeriya zai iya 'komawa gidan jiya' a karo na biyu cikin shekaru 4 - Buhari

Tattalin arzikin Najeriya zai iya 'komawa gidan jiya' a karo na biyu cikin shekaru 4 - Buhari

- A ranar Alhamis ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2021

- Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudi N13.1trn a gaban mambobin majalisar tarayya yayin wani zama na musamman

- Buhari ya bayyana cewa annobar korona da faduwar farashin danyen mai ta nakasa tattalin arzikin Najeriya

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce tattalin arzikin Najeriya zai iya sake komawa gidan jiya, watau cikin irin mawuyacin halin da ya taba shiga a baya.

Buhari ya bayyana hakan ne yayin da ya ke gabatar da kasafin kudin shekarar 2021 a gaban mambobin majalisar tarayya.

A ranar Alhamis ne shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2021 yayin wani zama na musamman da ya hada mambobin majalisar dattijai da na wakilai wuri guda.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa bullar annobar korona ya taba tattalin arzikin Najeriya, sannan ya kara da cewa faduwar farashin danyen mai ta hana gwamnati samun isassun kudin shiga.

DUBA WANNAN: Ta nan kudade su ke zirarewa: Majalisa ta shawarci Buhari ya soke wasu hukumomi

Buhari ya gabatar da kasafin kudi na N13.1trn, hakan ya nuna cewa an samu karin kaso 20% a kan adadin kudin da gwamnati ta yi kasafi a baya.

A cewar Buhari, akwai gibin N4.8trn a cikin kasafin, wanda ya bayyana cewa gwamnati za ta cike gibin da rance daga ketare.

Tattalin arzikin Najeriya zai iya 'komawa gidan jiya' a karo na biyu cikin shekaru 4 - Buhari
Shugaba Buhari yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2021
Asali: Twitter

"An yi hasashen cewa kudaden da gwamnati ta ke samu a cikin gida (GDP) za su ragu a watannin karshe na wannan shekarar da mu ke ciki.

DUBA WANNAN: Sai Murna: Buhari ya amince a bawa daliban da suka yi karatun NCE aiki, ya kara shekarun aikin malamai

"A saboda haka, tattalin arzikinmu zai iya sake komawa cikin wata masassarar a karo na biyu cikin shekaru hudu, wanda hakan zai zo da wasu wahalhalu.

"Sai dai, duk da haka, mu na aiki tukuru domin kirkirar hanyoyin farfado da tattalin arzikinmu a cikin shekarar 2021.

"Za mu mayar da hankali wajen kaddamar da shirye-shirye da za su bawa gwamnati damar tsamo 'yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10 ma su zuwa," a cewar Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng