PDP ta yi watsi da wanda aka naɗa babban baturen zaben Ondo saboda alaƙarsa da gwamna

PDP ta yi watsi da wanda aka naɗa babban baturen zaben Ondo saboda alaƙarsa da gwamna

- Jam'iyyar PDP ta yi watsi da nadin shugaban jami'ar Awolowo da ke Ile-Ife a matsayin baturen zabe na zaben gwamna da za a yi a ranar Asabar a Ondo

- Babban jam'iyyar hammayar ta ce bata yarda da nadinsa ba domin shi da gwamnan jihar mai ci duk 'yan karamar hukuma daya ne

- Har wa yau, PDP ta ce an dade da sanin cewa shi na hannun daman gwamna Akeredolu ne don haka ba zai yi adalci ba

PDP ta yi watsi da wanda aka nada babban baturen zaben Ondo saboda alakarsa da gwamna
Etiyope Ogunbodede. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masu garkuwa sun sace amaryar mai gidan burodi a Katsina

Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta ce bata amince da nada shugaban jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife, Farfesa Etiyope Ogunbodede a matsayin baturen zabe na zaben gwamna da za ayi ranar Asabar a jihar Ondo ba.

Shugaban kwamitin yakin neman zabe na kasa na PDP, wanda shine gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ne ya sanar da hakan yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Alhamis a Akure.

KU KARANTA: Yadda rundunar sojojin Najeriya za ta yi nasarar yaƙi da Boko Haram - Zulum

Makinde ya ce basu gamsu da nadinsa ba saboda Ogunbodede ya fito daga karamar hukuma daya da gwamnan jihar Rotimi Akeredolu na jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Ya kuma kara da cewa an dade da sanin cewa shugaban jami'an na hannun daman Gwamna Akeredolu ne don haka ba zai yi adalci ba a zaben.

A wani labarin daban, Shugaba Buhari ya bayyana goyon bayansa ga tazarcen da gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ke neman yi.

Gwamnan da aka zaɓa a karon farko a 2017 yana fatar zarce wa kan mulki idan al'ummar jihar sun dake zabensa a zaɓen da za ayi ranar Asabar 10 ga watan Oktoba.

Buhari, a ranar 7 ga watan Oktoba ya ce ya gamsu da irin kamun ludayin gwamnan kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: