NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi ta N1.2bn a arewa

NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi ta N1.2bn a arewa

- Jami'an hukumar NDLEA sun gano wata babbar gonar tabar wiwi a jihar Kogi

- Kwamandan NDLEA a jihar Kogi, Alfred Adewunmi, ya ce sun gano gonar ne ta hanyar samun bayanan sirri

- Hukumar NDLE ta ce gano babbar gonar a jihar Kogi da ke arewacin Najeriya ya basu matukar mamaki

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) ta ce ta samu nasarar lalata gonar tabar wiwi wacce darajar ta ya haura Naira biliyan ɗaya da rabi a garin Agbokete dake ƙaramar hukumar Igalamela-Adolu a jihar Kogi.

Da yake magana da manema labarai a ranar laraba, Alfred Adewunmi, kwamandan hukumar NDLEA na jihar Kogi, ya ce gonar mai kimanin tsawon kilomita huɗu sun gano inda ta ke ta hanyar tattara bayanan sirri daga jami'ansu.

Adewumi yace; ''a tsammaninmu Jihar Kogi wuri ne da ake shigo da Wiwi saboda irin yanayin da jihar ke da shi, sai dai labarin ya sha ban-ban saboda jihar tana ɗaya daga cikin masu nomanta.

"Ina faɗa muku cewa na yi matuƙar girgiza da kaɗuwa, kuma na razana da jin cewa abu ƙatoto babba kamar wannan za'a iya samunsa a jihar Kogi.

DUBA WANNAN: Ta nan kudade su ke zirarewa: Majalisa ta shawarci Buhari ya soke wasu hukumomi

"A tunaninmu, duk da jihar Kogi ta yi maƙwabtaka da jihohin da suka yi fice wajen noma ganyen tabar wiwi, mun ɗauka kawai jihar wurin wucewa da ita ne saboda sarƙaƙiyarta.

"Gaskiya gano cewa a cikin Jihar kogi akwai ƙatuwar gonar wiwi kamar wannan abu ne da ya girgiza ilahirin jikina.

NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi ta N1.2bn a arewa
NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi ta N1.2bn a arewa @lailanews
Asali: Twitter

"Gona ce mai matuƙar girma, dukkaninku kun shigo ayarina kuma kunga adadin tafiyar da muka shafe kimanin kilomita huɗu kuma har yanzu muna cikinta."

"in aka ce na bayyana abin da gani yau; zance nayi matuƙar razana da ganin irin yawan wiwin da ake sarrafawa a jihar nan."

"Yawan tabar wiwin da muka samu a yau ya nin-ninka wiwin da muka gano a tsakiyar watan satumba nesa ba kusa ba.

DUBA WANNAN: Ganduje zai gina makarantu na musamman a masarautun Kano 5

"Idan ku ka haɗa waɗannan gonaki wuri guda za ku ga cewa ya haura hekta 35 na wiwi a dunƙule.

"Idan kuwa za'a yi maganar kimar kuɗin, maganar gaskiya sunkai ko na ce sun fi biliyan ɗaya da rabi(₦1.5b)."

Kwamandan ya ƙara da cewa, Ameh joseph, mai mallakin wannan gonar zai gurfana gaban kuliya da zarar an kammala bincike.

Ya kuma gargarɗi masu noman wiwin da su daina, su tuba, su sauya sana'a tun kafin su shiga komar jami'an tsaro.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel