Ta nan kudade su ke zirarewa: Majalisa ta shawarci Buhari ya soke wasu hukumomi

Ta nan kudade su ke zirarewa: Majalisa ta shawarci Buhari ya soke wasu hukumomi

- Sanatoci sun shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya soke wasu hukumomi da ke zaman kawai

- Majalisar dattijai ta ce gwamnati ba za ta samu wasu manyan kudade ba idan aka rage kasafinta

- Gwamnatin tarayya na yawan korafin cewa ta na kashe makudan kudi wajen gudanar da ma'aikatu da hukumominta

Majalisar dattijai ta shawarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya soke wasu hukumomi da ke zaman kawai.

A cewar majalisar, hakan zai taimakawa gwamnati wajen rage yawan adadin kudaden gudanarwa da ta ke kashewa.

Wannan shawara na kunshe ne a cikin rahoton tsarin dabarun tafiyar da gwamnati daga 2021-2023 da majalisar dattijai ta amince da shi.

Shugaban kwamitin harkokin kudi a majalisar dattijai, Sanata Solomon Adeola, ne ya gabatar da rahoton a gaban majalisa.

Bayan mambobin majalisar sun amince da rahoton, shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, ya ce irin wadannan hukumomi sun zama hanyar zirarewar kudaden gwamnati.

DUBA WANNAN: Boko Haram: Rundunar soji ta karbi sabbin tankokin yaki da sabbin makamai na zamani

Lawan ya bayyana cewa majalisa za ta hada kai da bangaren zartarwa domin zakulo irin wadannan hukumomi.

"Da yawa daga cikin wasu hukumomi an kirkiresu ne domin wata matsala ko bukata a wani lokaci.

Ta nan kudade su ke zirarewa: Majalisa ta shawaci Buhari ya soke wasu hukumomi
Shugabannin majalisa da shugaba Buhari
Asali: UGC

"Yanzu basu da wani tasiri balle sauran katabus, sun zama hanyar zirarewar kudaden gwamnati duk shekara.

DUBA WANNAN: Sai Murna: Buhari ya amince a bawa daliban da suka yi karatun NCE aiki, ya kara shekarun aikin malamai

"Za mu hada kai da bangaren zartarwa domin zakulo irin wadannan hukumomi. Na san hakan zai haifar da rudani da cece-kuce.

"Ba aiki ne mai sauki ba, na san za a zargemu da yunkurin raba jama'a da aikinsu, amma ya zama dole mu nemi hanyar rage zurarewar kudaden gwamnati.

"Rage kasafin kudin majalisa ba zai karawa gwamnati wasu kudi ma su yawa ba, kasafin majalisa N128bn ne daga cikin kasafin kasa N13trn," a cewar Lawan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayarku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel