Jerin abubuwa 7 da Hizbah ta haramta a jihar Kebbi

Jerin abubuwa 7 da Hizbah ta haramta a jihar Kebbi

- Kamar a Kano, hukumar Hisbah a Kebbi ta kafa dokokin gyaran tarbiyya

- Hukumar na karkashin mai baiwa gwamna shawara kan lamarin addini

- Jihar Kebbi na daga cikin jihohin Arewa maso yammacin Najeriya

Kwamitin Hisbah dake karkashin ofishin mai baiwa gwamna shawara kan lamuran addini a jihar Kebbi ta gindaya abubuwan da aka haramtawa matasa da yan kasuwa yi a cikin garin Yauri, na jihar.

Hukumar a takardar da ta saki ta bayyana jerin abubuwan wanda ya hada tauye mudu, sa wando irin na yan gayu masu bayyana wani sashen duwawunsu a waje, da wasan kwallon kwamfuta PES.

Sauran abubuwan sun hada da daukan mace fiye da daya a babur, talla bayan Sallan magariba da aikin kide-kide.

DUBA NAN: Majalisar wakilai ta rincabe da hayaniya yayinda mambobi 2 suka sauya sheka daga PDP zuwa APC

Jerin abubuwa 8 da Hizbah ta haramta a jihar Kebbi
Jerin abubuwa 8 da Hizbah ta haramta a jihar Kebbi
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jihohi 9 ne masu arziki a Najeriya, 12 matsiyata ne kuma duk Arewa suke - Masanin Tattalin arziki

A wani labarin daban, Jami'an hukumar Hisbah a jihar Kano sun ladabtar da matasa inda suka dinga aske musu gashin kansu sakamakon askin da suka yi ba na Musulunci ba.

Sau da yawa jami'an hukumar Hisbah suna damke matasa a jihar Kano a kan laifin saka kaya ba yadda ya dace ba.

Su kan tsare masu adaidaita sahu da ke ado da hotunan mawaka ko jaruman fina-finai.

Lamarin nan da ya faru ya janyo cece-kuce daga kafafen sada zumuntar zamani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel