Allah ya yi wa DG na kungiyar dattawan arewa rasuwa

Allah ya yi wa DG na kungiyar dattawan arewa rasuwa

- Babban bango ya fadi a arewa, John Yima Sen, dattijon arewa ya rasu yana da shekaru 69 da haihuwa a asibitin Garki dake Abuja

- Sen babban malami ne a jami'ar Baze dake Abuja, inda ya koyar a fannin jaridanci, kuma ya tsaya tsayin-daka wurin bunkasa arewa

- Kafin rasuwarsa, ya rike mukamai manya a Najeriya, har da mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa, a lokacin mulkin Shehu Shagari

John Yima Sen, wani mai rajin kare hakkin bil-adama kuma Darekta janar na kungiyar dattawan arewa, ya rasu.

A wata takarda da kungiyar hadin kan kungiyoyin arewa ta gabatar, wadda mamacin yake jagoranta, ta nuna Sen ya rasu ranar Talata da yamma yana da shekaru 69.

Kamar yadda jaridar Premium times ta ruwaito, ya rasu ne a asibitin Garki dake Abuja.

"Kungiyar ta tura sakon ta'aziyyar ta ga iyalan mamacin, kungiyar dattawan arewa, jami'ar Baze, mutanen jihar Benue da 'yan Najeriya gaba daya. Hakika mutuwarsa babbar rashi ce ga arewa saboda taimakonsa.

"Muna mika sakon ta'aziyyar mu sannan muna fatan Ubangiji ya ba iyalansa hakurin jure rashinsa," kamar yadda takardar ta'aziyyar ta zo.

Sannan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a ranar Laraba yace hakika mutuwar Sen tayi matukar girgizasa.

A wata takarda ta'aziyyar da aka wallafa a shafinsa: "Mutum ne mai matukar mutunci. Ya sadaukar da rayuwarsa wurin tabbatar da cigaba a Arewacin Najeriya. Yayi iya kokarinsa wurin taimakon na kasa don cigaban kasa. Munyi mummunar rashi."

Mamacin dan jihar Benue ne, kuma babban malami ne a jami'ar Baze, inda ya koyar da jaridanci.

Sen ya karanta jaridanci a jami'ar Legas, jami'ar California a Los Angeles, jami'ar Amurika da kuma jami'ar Amsterdam a Netherlands.

Ya rike mukamin mai bada shawara na musamman akan harkokin siyasa a lokacin Shehu Shagari ne Shugaban kasa. Da sauran manyan mukamai a wurare daban-daban.

Muna fatan mutuwa zata zama hutu a gareshi.

KU KARANTA: Auren Hausawa: Dukkan abinda ya kamata a sani daga nema zuwa samun auren

Allah ya yi wa DG na kungiyar dattawan arewa rasuwa
Allah ya yi wa DG na kungiyar dattawan arewa rasuwa. Hoto daga Premium Times
Asali: UGC

KU KARANTA: An rasa rai 1 bayan rumfar kasuwa ta rushe a kasuwar Kurmi da ke Kano

A wani labari na daban, rahoto da muke samu a yanzu ya nuna cewa, Allah ya yi wa Sakataren Masarautar Kano, Alhaji Mahmudu Aminu Bayero, rasuwa.

Marigayin ya rasu ne a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoba, jaridar Aminiya ta Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel