Iyalai 12,000 za su amfana da tallafin tsabar kudi a jihar Kano

Iyalai 12,000 za su amfana da tallafin tsabar kudi a jihar Kano

- Kimanin iyalai 12,000 da kuma masu kananan sana'o'in dake jihar Kano zasu amfana da tallafin COVID-19, cewar wakilin UNDP Muhammad Yahaya

- Yace jihar Kano tayi amfani da Naira biliyan 460 wurin tallafawa masu kananan karfi da sana'o'i dake kananan hukumomi 44 a Kano

- Ya kara da cewa, sun yi wannan shirin ne don tabbatar da gwamnati ta tallafawa wadanda suka durkushe sakamakon annobar Coronavirus

Kimanin iyalai 12,100 da kuma masu kananan sana'o'i na jihar Kano zasu amfana da tallafin COVID-19 a jihar, a cewar wakilin UNDP Muhammad Yahaya.

Kamar yadda wakilin UNDP, Muhammad Yahaya ya bayyana, an bada wannan tallafin ne don taimakon 'yan jihar.

Yahaya yayi maganar ne a wani taro da aka yi a gidan gwamnatin jihar Kano ranar Litinin, ya ce UNDP, WFP da EU ne suka dauki nauyin bada tallafin.

Kaddamar da shirin yazo daidai da fara shirin SDG a Kano, wadda zasu bada gadajen asibiti 200 tare da katifu, matasan kai, motoci 2 da takunkumin fuska 20,000 da sauran kayayyakin amfanin cibiyoyin lafiya.

A cewarsa, "UNDP da taimakon asusun UN COVID-19 sun taimaki mutane da dama, wadanda suka durkushe sakamakon annobar Coronavirus,"

Ya mika godiyarsa ga Gwamna Ganduje saboda taimakon da yayi ta bayar wa ga masu kananan karfi.

"Wannan shirin ya taimakawa iyalai 9,600 da masu kananun sana'o'i 2,500 da Naira miliyan 460 a jihar Kano. A cikin Naira biliyan 13 da aka ware don tallafawa 'yan Najeriya," kamar yadda ya bayyana.

Ya kara da cewa, "Fiye da gidaje 300,000 a gundumomi 484, tsakanin kananan hukumomi 44 na jihar sun amfana da wannan tallafin."

KU KARANTA: ISWAP ta sako manyan jami'an jihar Borno 5 da ta yi garkuwa da su

Iyalai 12,000 za su amfana da tallafin tsabar kudi a jihar Kano
Iyalai 12,000 za su amfana da tallafin tsabar kudi a jihar Kano. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Rikici kadan ke hada mu ta dinga zazzabga min mari - Magidanci ya sanar da kotu

A wani labari na daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana yadda gwamnatinsa ta tanadi zinari mai kimar Naira Biliyan 5 ga abokan kasuwancinsu na kasar waje.

Zailani Bappa, mai bai wa gwamnan shawara akan yada labarai, ya bayyana hakan ga manema labarai a wata takarda a Gusau, babban birnin jihar.

Matawalle ya bayyana yadda dama yake da yarjejeniyar sayar wa wasu abokan kasuwancinsu dunkulen zinare na Naira biliyan 5 da dadewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel