Auren Hausawa: Dukkan abinda ya kamata a sani daga nema zuwa samun auren

Auren Hausawa: Dukkan abinda ya kamata a sani daga nema zuwa samun auren

- Hausawa suna da al'adu masu bada sha'awa idan aka zo batun aure

- Duk da musulinci ya canja al'adu da dama na auren Malam bahaushe

- Amma a fagen birgewa da kayatarwa, auren hausawa ya cire tuta

Al'adu na biyo bayan daurin aure a musulunce. Akwai tabbacin mutane da dama sun yi ta ganin hotunan bikin auren hausawa, kuma anyi ta burin sanin yadda al'ada ta tanada.

Anan zamu kawo muku yadda Hausawa ke al'adunsu masu ban sha'awa idan shagalin aure ya tashi. Ana fara yin wasu al'adu kafin daurin aure, wasu al'adun kuma suna biyo bayan daurin aure.

1. Kayan Zance

Sune kayan da dangin saurayi ke gabatarwa ga dangin budurwar da yake so ya aura don kowa yasan yana neman aurenta.

Abubuwan da zasu kawo sun hada da kayan kicin, kayan kwalliya, takalma, kudin gaisuwa da makamantansu.

Idan dangin angon suna da hali, akan bukaci su bayar da gidan da mijin zai ajiye matarsa. Idan hakan ta faru, wajibi ne dangin amarya su yi mata duk wasu kayan daki, falo, da kuma kicin.

Anayin duk wadannan abubuwan ne kafin daurin aure.

2. Daurin Aure

Shafa Fatiha tafi komai muhimmanci a gabadaya sha'anin. Hausawa da dama su kan bayyanar da wakilin ango daga dangi ko 'yan uwa da abokan arzikinsa.

Sai waliyyin amarya wanda zai bayar da aurenta. Zai iya zama mahaifinta ko kuma wani makusancinta.

Sai Limami wanda shi zai daura auren sannan ya gabatar da addu'o'in zaman lafiya ga ma'auratan. Anayin hakanne kamar yadda addini ya tanadar.

3. Sa Lalle

Mata ne kadai suke yin wannan. Shine lokacin da amarya ke samun damar hira da kawayenta hade da barkwanci, a gidan mahaifinta.

Ana kwaba lalle don ayi wa amarya da kawayenta ado na musamman a hannayensu da kafafu.

Amma dole ne lallen Amarya ya banbanta da na kowa, a wurin yawa da kyau, musamman na hannayenta. Hakan na biyo bayan ciye-ciye da kawayen amarya da amaryar zasu yi.

4. Kamun Amarya

Kamu dadaddiyar al'adar hausawa ce. Kuma tana daukan hankalin jama'a da dama. Ana ciniki ne tsakanin dangin Ango da Amarya don a sakar musu amaryar su.

Kudin da dangin Ango za su bayar ya danganta da yanayin arzikin su. Anayin cinikin cikin nishadi da barkwanci na tsawon minti 30, tukunna a ci a sha.

5. Siyan Baki

A wasu wuraren, akanyi al'adar nan don ta karawa bikin armashi. Siyan baki wata al'adace wadda za'ayi ciniki tsakanin abokan Ango da kawayen amarya kafin kawayen su bar Ango ya gana da Amaryarsa.

6. Kai Amarya

Dangin Amarya da kawayenta suna rakata gidan mijinta, inda dangin Ango ke tarbarsu. Daga nan ne ake taya su da addu'o'i da kuma nasihohi.

Wannan bashi bane karshen al'adun hausawa ba a wurin bikin aure ba.

Duk da dai ya danganta da arzikin danginsu, tun da ana gabatar da kayan ciye-ciye, kade-kade da kuma nishadi.

KU KARANTA: Dalilin da yasa na yi nadamar taya Buhari kamfen a 2015 - Tsoho mai shekaru 80

Auren Hausawa: Dukkan abinda ya kamata a sani daga nema zuwa samun auren
Auren Hausawa: Dukkan abinda ya kamata a sani daga nema zuwa samun auren. Hoto daga The Pulse
Asali: UGC

KU KARANTA: Magidanci ya sanya wa jaririnsa suna Buhari saboda karrama shugaban kasa (Hotuna)

A wani labari na daban, wani bidiyon amaryar da ta tsere ranar aurenta bayan ta gano saurayin da zata aura yana tarayya da kawarta ya karade kafafen sada zumunta. Al'amarin ya faru ne a Area 2, a Garki jihar Abuja.

Kamar yadda aka wallafa a shafin sada zumunta, wata mata na cikin mota zata nufi wurin daurin aurenta, kwatsam sai aka kirata a waya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel