Rikici kadan ke hada mu ta dinga zazzabga min mari - Magidanci ya sanar da kotu

Rikici kadan ke hada mu ta dinga zazzabga min mari - Magidanci ya sanar da kotu

- Wani bakanike mai suna Olumayowa Afolabi ya maka matarsa a kotu saboda duka da marin da take yi masa

- Ya ce matar ta sa ta taba yi masa tsirara, ta kuma zane ma sa jikinsa akan ya hana ta fita da daddare amsar wayarta

- Ya kara da cewa tana marinsa har a gaban kannin ta inda har kannin nata sun sha ja mata kunne

Wani bakanike, Olumayowa Afolabi ya roki kotun Ile-Tuntun dake Ibadan ranar Talata da ta tsinke igiyar aurensa na shekara 17 da matarsa, sakamakon rashin daraja sa da kuma yunkurin kashe shi.

Mutumin mazaunin layin Odeyan-Akanran a Ibadan ya sanar da kotun yadda ya gaji da zama da matarsa saboda marinsa da ta ke yi akai-akai.

"Mai girma mai shari'a, idan da wani zai fada min cewa Mojisola zata dinga dukana, da na karyata shi.

"Ta fara mari na ne a 2018 lokacin akan nayi mata magana akan dambe da tayi da wasu malamai 4 dake zama a gidanmu. Tun daga lokacin tana mari na duk sanda muka samu matsala.

"Sakamakon sabawa da tayi da mari na, tana yi har a gaban kanninta, wanda su da kansu sun sha ja mata kunne akai.

"Wanda yafi kona min rai shine yadda ta yi min tsirara ta kuma zaneni a watan Mayu, saboda na hana ta fita amsar wayarta da daddare.

"Ta riga ta nuna min karara cewa ta daina so na, kuma bata bukatar zama dani," cewar Olumayowa.

Sai dai Mojisola ta roka kotu da kada ta rabata da mijinta, ta ce wata kawarta ce ke kokarin lalata mata aurenta. Ta musanta marin sa.

Ta ce, wata kawarta kuma 'yar cocinsu, mai suna Esther Oluremi, wadda mijinta yaba kiwon kaji ce matsalar aurensu.

Ta ce, "Mijin matar ya koreta daga gidansa, da muka ziyarceta ranar 1 ga watan Janairu na ga Olumayowa yana shafa mata hoda a fuskarta. Wannan ne dalilin da yasa nake azabtar dashi."

Bayan alkali Henry Agbaje ya gama sauraron shari'ar, ya ce alakarsu ta samu mummunar tangarda, don haka dole ne a kwance igiyar aurensu.

KU KARANTA: Osinbajo ya kalubalanci tsarin da FG take bi wurin nade-nade

Rikici kadan ke hada mu ta dinga zazzabga min mari - Magidanci ya sanar da kotu
Rikici kadan ke hada mu ta dinga zazzabga min mari - Magidanci ya sanar da kotu. Hoto daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Babban ci baya ne gareni idan aka bukaci in zama shugaban kasa - Bishop Oyedepo

A wani labari na daban, hakika duk uwa tagari tana wahala wurin taso da ya'yanta tun yarinta har girmansu. Sai dai ace Allah ne zaiyi sakayya kawai.

Bidiyon wata mata mai sana'ar fenti, mai suna Sognan Silla ya karade kafafen sada zumuntar zamani, inda aka ga matar tana sana'arta goye da jaririnta.

A bidiyon, matar na tsaye akan wani benci tana shafawa silin din wani daki fenti. Hakika bidiyon ya karade kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, wanda fiye da mutane 400,000 suka gani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel