FG ta bada umurnin sake tantance masu N-Power

FG ta bada umurnin sake tantance masu N-Power

- Gwamnatin Tarayya ta umurci masu amfana da shirin aikin matasa na N-Power da ba su samu allawusi dinsu ba su tafi a tantance su

- Gwamnatin ta ce tantancewar ya zama dole ne domin an gano akwai wasu da ke karbar albashi a maaikatun gwamnati kuma su karbi na N-Power

- An umurci wadanda za su tafi tantancewar su tafi da wasu muhimman takardu kuma za a kammala a ranar 13 ga watan Oktoba

FG ta bada umurnin sake tantance masu N-Power
FG ta bada umurnin sake tantance masu N-Power. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kishi ya saka ango ya kashe amaryarsa da duka a wurin bikin aurensu a Rasha

Gwamnatin tarayya ta bada umurnin masu amfana da shirin N-Power na Batch A da B da ba su samu kudadensu na watanni baya ba su tafi ofisoshin wakilansu na jihohi domin sake tantance su.

Ministan jin kai da kare afkuwar balai, Sadiya Umar Faruk ce ta bada wannan umurnin a ranar Talata kamar yadda ThePunch ta ruwaito.

Ta ce an bada umurnin ne domin warware wasu matsaloli da ke suka janyo jinkiri wurin biyan wasu daga cikin masu N-Power din.

KU KARANTA: Matsalolin Najeriya: Rashin tunani zai sa a dora wa mulkin soja laifi - Babangida

A cewarta, binciken da ofishin Akanta Janar na kasa ta yi bayan wasu sun koka cewa ba su samu allawus dinsu ba ya nuna akwai wasu da ke karbar albashi daga maaikatun gwamnatin tarayya kuma suka karbar allawus na N-Power.

Ministan ta ce wannan tantancewar za ta bawa wadanda abin ya shafa dama su tantance sahihancinsu domin a cigaba da biyansu allawus dinsu da suka yi saura.

"Ana umurtar masu amfana da shirin N-Power su tafi ofisoshin jihohinsu tare da lamban asusun bankunansu, har da takardar hada hadar bankinsu tun daga watan Maris zuwa yanzu, takardar shaidar kammala NYSC, takardan shaidan haihuwa da sauran takardu don a tantance su," inji Faruk.

Ta ce a ranar 13 ga watan Oktoban 22 za a dakatar da aikin tantancewar.

Ministan ta kuma ce dukkan wadanda ba su hallarci tantancewar ba ba za su samu allawus dinsu ba.

A wani labarin daban,Shugaba Muhammadu Buhari ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan Aliu, masana'antar masu nishadantarwa da gwamnatin jihar Ekiti bisa rashin fitaccen mai wasan drama, Jimoh Aliu. Jimoh Aliu ya rasu yana da shekaru 80a duniya kamar yadda The Pulse ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel