Dalilin da yasa na yi nadamar taya Buhari kamfen a 2015 - Tsoho mai shekaru 80
- Wani dattijon basarake mai shekaru 80 a duniya ya bayyana nadamarsa ta zaben Buhari
- Ya ce ya yi matukar nadama da ya shiga sahun masu gangamin neman zaben Buhari a 2015
- Basaraken ya ce Buharin da ya sani a yayin mulkin soja ba shi bane a halin yanzu
Basarake a jihar Ogun, Joseph Ogunfuwa, ya nuna nadamarsa na yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kamfen a 2015.
Ogunfuwa wanda ke da sarautar Babalaje na Remoland a jihar Ogun, ya ce Buhari ya bashi kunya tare da yawan 'yan Najeriya.
Ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da yayi ga jama'a a Sagamu domin bikin cikarsa shekaru 80 a duniya.
Ogunfuwa ya ce Buhari da ya sani ba shi bane na yanzu da yake gani.
"Abinda na fi nadama a rayuwata shine yadda na dinga gangamin neman zabensa a 2015. Na bayyana tabbacina a kan cewa shine kadai zai iya mulkar kasar nan kuma ya cetota.
"Wasu daga cikin abokaina sun bar ni suna zaton na haukace ne. Sun ce a yanzu farar hula ne ba soja ba. Dan siyasa ne kawai.
"A yau na gane cewa na tafka babban kuskure. Shugaban kasa, kana da shekaru biyu da rabi da za ka inganta rayuwar 'yan Najeriya. Wannan shine sakona ga 'yan siyasa, sanatoci, musulmi da kiristoci," yace.
KU KARANTA: Bidiyon amaryar da ta tsere ranar bikinta bayan gano boyayyen sirrin angonta

Asali: Twitter
KU KARANTA: Sama da shekaru 7 nake rufa wa matata asiri saboda darajar 'ya'ya - Fani Kayode
A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Lahadi ya nuna fushinsa a kan kame da cin zarafin da jami'an 'yan sanda suke wa matasa a Najeriya.
Mataimakin shugaban kasan wanda ya samu zantawa da Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ya sanar da shugaban 'yan sandan da ya kawo sauye-sauye da za su canza miyagun ayyukan 'yan sandan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng