Edinson Cavani, Alex Telles, Facundo Pellistri, Amad Diallo sun tafi Manchester

Edinson Cavani, Alex Telles, Facundo Pellistri, Amad Diallo sun tafi Manchester

- Manchester United ta kashe kudi wajen sayen sababbin ‘yan wasan kwallo hudu

- Kungiyar ta koma kasuwa gadan-gadan ne bayan tsohon Kocinta ya ci ta har 6-1

- Edinson Cavani, Alex Telles, Facundo Pellistri, Amad Diallo za su bugawa United

Sky Sports ta tabbatar da cewa kungiyar Manchester United ta saye ‘yan wasan kwallon kafa hudu kafin a rufe cinikin ‘yan wasa a kasar Turai.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Tottenham ta ragargaji Manchester United a Old Trafford.

Tsohon ‘dan wasan gaban kungiyar PSG Edinson Cavani shi ne mafi shahara a cikin sababbin ‘yan wasan da kungiyar ta sayo a ranar Litinin.

‘Dan wasa Edinson Cavani mai shekaru 33 zai rattaba hannu a kan kwangilar shekara guda, tare da yiwuwar kara shafe wata shekara a kulob din.

KU KARANTA: Barcelona ta rabu da Taurari 4 a wata 1

Alex Telles ya tabbatar da cewa ya bar kungiyar FC Porto zuwa Manchester United, an kashe fam £15.4m wajen sayen ‘dan wasan na kasar Brazil.

‘Dan wasan gaban kungiyar Atalanta, Ahmad Diallo zai koma wasa a Old Trafford, Diallo zai cigaba da zama a Italiya har zuwa watan Junairu.

Bayan nan kungiyar Manchester United ta saye ‘dan wasan kasar Uruguay mai tasowa, Facundo Pellistri a kan kudi kusan fam miliyan £10 a jiya.

Edinson Cavani, Alex Telles, Facundo Pellistri, Amad Diallo sun tafi Manchester
'Yan wasan Manchester Hoto: Man Utd.
Asali: UGC

KU KARANTA: Messi ya yi nasara a shari'arsa a kotu

Ana sa ran cewa tsohon ‘dan wasan gaban na PSG Cavani zai goya lamba 7 a rigarsa. Zai bi sahun ‘yan wasa David Beckham da Cristiano Ronaldo.

Kafin nan Ole Gunnar Solskjaer ya yi kokarin sayen Jadon Sancho daga kungiyar Dortmund.

Ku na da labari cewa a kasuwar bana, kungiyar Liverpool ta saye 'dan wasan tsakiya, Thiago Alcantara, daga kungiyar Bayen Munich ta kasar Jamus.

Haka kuma Barcelona ta yi wa Atletico Madrid gwanjon Luis Suarez, ta kuma saye Sergino Dest.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel