Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2021 ranar Alhamis

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2021 ranar Alhamis

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya zabi ranar bayyana gaban yan majalisa

- Majalisar zartarwar tarayya ta Najeriya ta amince da fitar da tiriliyan N13.08 a matsayin kasafin kudin 2021

- Buhari ya kebe bilyan goma don shirye-shiryen kidayan yan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari yana neman izinin gabatar da kasafin kudin 2021 gaban majalisar dokokin tarayya ranar Alhamis, 8 ga Oktoba, 2020.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar da shugaba Buhari ya aikewa majalisar da safiyar Talata a zauren majalisa.

KU KARANTA: Shirin lamunin abincin duniya WFP ta fara raba kudi da abinci ga mutane 67,000 a Kano

A baya mun kawo muku rahoton cewa majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) wacce shugaban kasa Muhammadu Buhari yake jagoranta a taronta na yau Laraba, ta amince da fitar da tiriliyan N13.08 a matsayin kasafin shekarar 2021.

Ministan kudi, kasafi da tsarin kasa, Hajiya Zainab Ahmed ce ta sanar da hakan a wani taro na manema labarai akan abinda majalisar zartarwar ta zartar a taron da aka yi a wani dakin taro dake fadar shugaban kasa, Abuja.

Hajiya Zainab tare da Minsitan yada labarai da al'adu, Lai Muhammed; karamin Ministan kasafi, tsari da tattali, Clement Agba da darakta janar na ofishin kasafin kasa, Ben Akabueze ne suka yi bayanin.

Ministan tace gaba daya kasafin shekarar ya kama tiriliyan N2.083, yayin da kudin kowacce gangar man fetur ake tammaninsa a dala 40, Daily Trust ta wallafa.

Duba nan; Ku maye gibin kujerun yan majalisar APC jihar Edo - PDP ga INEC

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel