Bude Makarantu: Shugaban ASUU ya ce Malamai ba za su yi aiki cikin yunwa ba

Bude Makarantu: Shugaban ASUU ya ce Malamai ba za su yi aiki cikin yunwa ba

- Kungiyar ASUU ta yi magana game da yajin aiki da shirin bude Makarantu

- Shugaban ASUU ya ce an yi watanni uku zuwa takwas ba a biyansu albashi

- Biodun Ogunyemi ya bayyana cewa ba su bude ofis a irin wannan yanayi ba

Alamu su na nuna cewa idan ranar bude makarantu ta zo a Najeriya, za a samu jami’o’in gwamnatin tarayya a rufe saboda yajin aikin ma’aikata.

Kungiyar ASUU ta malaman jami’a, ta yi watsi da umarnin da gwamnatin tarayya ta bada na cewa a koma bakin aiki a ranar 12 ga watan Oktoba, 2020.

Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Biodun Ogunyemi ya shaidawa jaridar Punch cewa gwamnati ba da gaske ta ke wajen kawo karshen yajin-aikinsu ba.

A wata hira ta wayar salula, Farfesa Biodun Ogunyemi ya ce ‘yan ASUU ba za koma aji da yunwa ba, sakamakon watanni da su ka yi ba a biyansu albashi.

KU KARANTA: Adamawa da Gombe sun fadi ranakun bude Makarantu

Biodun Ogunyemi ya soki Akanta-janar na kasa, Ahmed Idris, na sabawa umarnin da shugaban kasa ya bada na cewa a biya malaman makaranta albashinsu.

Farfesan ya nuna cewa a shiryawa dogon yajin-aiki a sakamakon salon da gwamnati ta dauka.

Shugaban na ASUU ya tabbatarwa manema labarai cewa malaman jami’a ba za su koma aji a yanayin da ake ciki ba, rabon wasunsu da albashi tun Fubrairu.

“Ba ku sa ran cewa mutane su koma ofis su zauna da yunwa. Ba ku sa ran ‘yan kungiyarmu za su dakatar da yaji yayin da ba a biya bukatunsu ba.” Inji sa.

KU KARANTA: Rashin albashi ya sa Malamin Jami’a ya kashe kansa da kansa

Bude Makarantu: Shugaban ASUU ya ce Malamai ba za su yi aiki cikin yunwa ba
Shugabannin ASUU a taro Hoto: This Day
Asali: UGC

Farfesan ya ce tun Agusta su ka rubutawa gwamnatin tarayya takarda cewa sun yarda ayi amfani da manhajar UTAS maimakon IPPIS wajen biyansu albashi.

Ya ce gwamnatin tarayya ba ta ba ASUU amsa ba sai bayan fiye da kwanaki 40. A cewarsa da gangan ake yin wannan domin a fusata kokarin malaman jami’a.

Farfesa Ogunyemi ya ce duk wanda ya shiga cikin rigar kungiyar ASUU, abin da zai yi kenan.

Ana cikin wannan yanayi kuma kungiyoyin SSANU da NASU sun fito su na kokawa a kan manhajar IPPIS da aka kawo wajen biyan albashi a gwamnati.

Ma’aikatan Jami’an sun tafi yajin-aiki lokacin da ake shirin bude makarantu a Oktoban nan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel