Osinbajo ya magantu a kan yadda jami'an SARS ke azabtarwa da kashe 'yan Najeriya

Osinbajo ya magantu a kan yadda jami'an SARS ke azabtarwa da kashe 'yan Najeriya

- Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasar Najeriya ya ca ya fusata da ayyukan jami'an SARS a kasar nan

- Kamar yadda ya bayyana ga manema labarai, ya zanta da sifeta janar na 'yan sandan Najeriya a kan hakan

- Mataimakin shugaban kasan ya bukaci a zakulo tare da ladabtar da duk jami'in da aka kama da laifin zalunci

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Lahadi ya nuna fushinsa a kan kame da cin zarafin da jami'an 'yan sanda suke wa matasa a Najeriya.

Mataimakin shugaban kasan wanda ya samu zantawa da Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ya sanar da shugaban 'yan sandan da ya kawo sauye-sauye da za su canza miyagun ayyukan 'yan sandan.

KU KARANTA: Hotuna da bidiyon motar N460 miliyan da Dino Melaye ya siya

Farfesa Osinbajo ya kara da sanar da Adamu cewa, ya tabbatar da an ladabtar da duk jami'in dan sandan da aka kama da cin zarafin ko kashe matasa a kasar nan.

A yayin amsa tambayoyin manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ya ce, "Na yi matukar damuwa kuma na fusata da abinda ke faruwa da matasa maza da mata. A wasu lokutan ana azabtar da su har ta kai ga kisa."

Osinbajo magantu a kan yadda jami'an SARS ke azabtarwa da kashe 'yan Najeriya
Osinbajo magantu a kan yadda jami'an SARS ke azabtarwa da kashe 'yan Najeriya. Hoto daga @Vanguard
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bakar ranar ga Boko Haram: Dakarun soji sun ragargaza maboya da wasu 'yan ta'adda a Borno

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sanda, M.A Adamu ya dakatar da ma'aikatan FSARS daga cigaba da ayyukansu, sakamakon korafin da 'yan Najeriya suke yi akan 'yan sanda na ta'addanci.

Ba su kadai wannan umarnin ya shafa ba, har da ma'aikatan STS, IRT da kuma ACS. An dakatar da ma'aikatan daga yin ayyuka kamar sintiri, tsayawa bincike, ba da hannu da sauran ayyukan da suke yi a kan tituna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel