Yadda Jami’ar Tayo Akpata ta rasa babban Malaminta, Friday Orobator
- Wani Malamin Makaranta ya kashe kan sa a jihar Edo saboda tsananin rashi
- Friday Orobator ya shafe wata da watanni Gwamnati ba ta biya sa albashi ba
- Wannan Bawan Allah ya gaji da rokon jama’a kudi, don haka ya rataye kansa
Friday Orobator, wani babban malami a tsohuwar kwalejin ilmin da yanzu ya zama jami’ar Tayo Akpata, a Ekiadolor, jihar Edo ya kashe kansa.
Premium Times ta fitar da rahoto a karshen makon da ya gabata cewa jama’a sun tsinci gawar Friday Orobator ne da rana ta tsaka a bayan gidansa.
Marigayin ya na zaune ne a unguwar Obakhazbaye da ke cikin babban birnin Benin, jihar Edo.
KU KARANTA: ASUU ta ce an hana Malaman Jami’a albashi na watanni 7
Jaridar ta ce Mista Orobator mai shekaru kusan 50 ya rataye kansa da igiya ne har ya mutu.
Mummunar mutuwar wannan Bawan Allah ta jawo na-kusa da kuma makwabta sun girigiza. Orobator ya na koyarwa ne a sashen karatun manya.
Rahoton ya nuna cewa marigayin ya dade ya na yi wa abokan aikinsa kukan ya na neman kudi domin ya samu ya yi maganin cutar da ke damunsa.
A ranar Larabar da ta wuce, Orobator ya fadawa wani abokin aikinsa cewa ya gaji da rokon jama’a kudi domin ya yi jinya da kuma dawainiyar iyalinsa.
Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa malaman jami’ar Tayo Akpata sun shafe fiye da shekara guda ba tare da gwamnatin jihar Edo ta biya su albashi ba.
KU KARANTA: IGP ya dauki dakarun 'Yan Sanda aiki, Alkali ya ce an saba dokar kasa
“Gaskiya ne, kowa ya san cewa mu na bin gwamnatin jihar Edo albashin watanni 13, wanda mu ka dade mu na nema tun ma kafin zabe.” Inji majiyar.
Malamin ya ke ba ‘yan jarida labari ranar Asabar: “Mai dakinsa (Marigayin) ta haifi jariri ba dadewa ba. Mun yi mamaki da mu ka ji jiya ya kashe kansa.
Malaman makarantar sun ce su na cikin wani yanayi maras dadi ganin yadda wannan Bawan Allah ya mutu ya bar ‘ya ‘ya hudu da mata guda mai jego.
A makon jiya kun ji labarin wani Matashi da ya yi yunkurin aika kansa lahira, ganin cewa Duniya ta yi masa zafi, ya rasa inda zai shiga domin ya ji sa'ida.
A karshe jami'an tsaro sun yi ram da shi zuwa gaban kotu, inda aka bada belinsa a kan N200, 000.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng