Bakar ranar ga Boko Haram: Dakarun soji sun ragargaza maboya da wasu 'yan ta'adda a Borno

Bakar ranar ga Boko Haram: Dakarun soji sun ragargaza maboya da wasu 'yan ta'adda a Borno

- Hedkwatar tsaro ta kasa ta tabbatar da ragargazar da mayakan Boko Haram suka fuskanta

- Dakarun sojin sun ragargaza maboyar 'yan ta'addan a ranar zagayowar 'yancin kan Najeriya

- Hakan ta faru ne a Maima da Tusuy da ke Warshale da Tongule a Dikwa-Rann ta Borno

Hedkwatar tsaro ta ce dakarun sojin saman Operation Lafiya Dole ta samu babban nasara ta hanyar halaka tushe da maboyar 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas a ranar bikin zagayowar cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai.

Shugaban fannin yada labarai na rundunar, John Enenche, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Manjo Janar Enenche, ya ce a ranar 1 ga watan Oktoba, dakarun sojin sun kashe 'yan ta'adda masu tarin yawa da maboyarsu a Maima da Tusuy kusa da Warshale da Tongule a yankin Dikwa-Rann da ke Borno.

Ya ce nasarar an sameta ne bayan bayanan sirri da suka samu wanda ya bayyana inda 'yan ta'addan suke kuma suke samun mafaka.

Kamar yadda yace, dakarun sojin saman sun yi amfani da jiragen yaki masu dauke da bindigogi inda aka ragargaza wuraren buyarsu biyu.

KU KARANTA: Nigeria @ 60: Ministan Buhari ya tabbatar da cewa ba zai yuwu a raba Najeriya ba

Bakar ranar ga Boko Haram: Dakarun soji sun ragargaza maboya da wasu 'yan ta'adda a Borno
Bakar ranar ga Boko Haram: Dakarun soji sun ragargaza maboya da wasu 'yan ta'adda a Borno. Hoto daga @DefenseInfoHQ
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya tabbatar da tabarbarewar tattalin arziki da tsaro a Najeriya

A wani labari na daban, samamen da dakarun sojin sama na rundunar Operation Lafiya Dole karkashin Operation Hail Storm 2 suka aiwatar suke aiwatar ya cigaba da bada sakamako mai kyau.

Na karshen da ya faru shine ragargaza sansanin mayakan ta'addanci da kuma halaka wasu daga cikin 'yan Boko Haram da ke Tongule, Bone da Isari B Musa a ranar 24 ga watan Satumban 2020.

Samamen da dakarun suka kai Tongule an kai shi ne sakamakon tabbacin da suka samu na cewa 'yan ta'addan na zama a yankin da dare kadai.

Kamar yadda ya dace, jiragen rundunar sojin saman dauke da bindigogin yaki sun kai hari yankin da dare, inda suka halaka da yawa daga cikin 'yan ta'addan.

A Bone, kusa da yankin Yale-Kumshe, jiragen yakin sun kai samamen bayan tabbataccen bayanin sirri da suka samu.

Jiragen dakarun sojin saman sun sakarwa yankin bama-bama tare da zuba musu ruwann wuta, lamarin da yasa sansanin da wasu mayakan suka halaka.

Hakazalika, a Isari B Musa, da yawa daga cikin 'yan t'addan sun mutu sakamakon harin ba-zata da jiragen yaki suka kai dajin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel