Daga ƙarshe: Ambasada Wali ya amince ayi sulhu tsakaninsa da Kwankwaso

Daga ƙarshe: Ambasada Wali ya amince ayi sulhu tsakaninsa da Kwankwaso

- Jigon jam’iyyar PDP a jihar Kano, Ambasada Aminu Wali, ya yarda da sulhu a tsakaninsa da Rabiu Kwankwaso

- Sai dai Wali ya ce wajibi ne a bi kundin tsarin mulkin jam’iyyar ta hanyar ba jama’a damar zabar wadanda suke so ba wai a tursasa masu wanda basa so ba

- Ya ce dole a ne a ba kan kowani dan jam’iyya yancinsa kamar yadda damokradiyya ta tanadar

Daya daga cikin manyan kusoshin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Kano, Ambasada Aminu Wali ya ce, ya yarda ayi sasanci a tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Hakazalika, Wali ya gindaya sharadin bisa kasancewar hakan, inda yace dole ne abi kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP wanda jama’ar da aka samu a basu damar zabar wadanda suke so.

Cewa ba wai shugaban jam’iyya ko wani ya yi musu kutse ba wajen dagewa kan wanda zasu zaba ba.

Daga ƙarshe: Ambasa Wali ya amince ayi sulhu tsakaninsa da Kwankwaso
Daga ƙarshe: Ambasa Wali ya amince ayi sulhu tsakaninsa da Kwankwaso Hoto: Premium Times/TheCitizen
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Bar murna karenka ya kama kura: Ƙusan APC ya ƙalubalanci nasarar Obaseki

Jigon na PDP ya bayyana hakan ne a cikin shirin ‘Kowanne Gauta’ na tashar Freedom Radiyo.

Aminu Wali yace "matukar jama’a suna sanka kuma sun zabeka ko ba kada ko sisi dole ayi da kai domin hakan shine Demokradiyya."

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Elrufai ya soke zaɓin farko na masu zaɓen Sarkin Zazzau

A wani labarin kuma, Jam'iyyar adawa ta PDP ta karyata zargin cewa tayi watsi da dan takaranta a zaben shugaban kasan 2019, Atiku Abubakar, domin zaben wani a 2023.

Daily Sun ta ruwaito cewa shugaban uwar jam'iyyar, Uche Secondus, ya karyata labarin bayan ganawarsa da wasu gwamnonin jam'iyyar a Bauchi.

Secondus ya ce jam'iyyar za ta tabbatar da cewa duk wanda ya cancanci takara zai iya ba tare da tsangwama ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel