Muna rayuwa cikin bala'i, Gwamnan Niger ya koka ga Buhari

Muna rayuwa cikin bala'i, Gwamnan Niger ya koka ga Buhari

- Gwamna Abubakar Bello na jihar Niger ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Asabar 2 ga watan Oktoba

- Gwamnan ya koka wa Shugaban kasar kan yadda titunan gwamnatin tarayya na jihar suka lalace wadda hakan ya jefa rayuwan mutane cikin bala'i

- Ya kuma nemi taimakon gwamnatin tarayya saboda barnar da ambaliyar ruwa ta yi wa manoma a jihar musamman manoman rake

Muna rayuwa cikin bala'i, Gwamnan Niger ya koka ga Buhari
Muna rayuwa cikin bala'i, Gwamnan Niger ya koka ga Buhari. Hoto: @BayoOmoboriowo
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya

Gwamnan jihar Niger, Abubakar Bello a ranar Juma'a ya koka wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa mutanen jiharsa na rayuwa cikin bala'i saboda lalacewar tituna da ambaliyar ruwa ya kara lalata su.

Ya gana da shugaban kasar a fadarsa da ke Abuja inda ya nemi gwamnatin tarayya ta kawo ma al'ummar jiharsa dauki don yaye musu bala'in da ke adabar su.

Yayin da ya ke magana da 'yan jarida bayan ganawarsa da shugaban kasar, ya ce rashin kyawun titunan gwamnatin tarayya yana barazana ga rayuwar mutane kuma hakan na iya raba su da sauran sassan kasar.

Muna rayuwa cikin bala'i, Gwamnan Niger ya koka ga Buhari
Muna rayuwa cikin bala'i, Gwamnan Niger ya koka ga Buhari. Hoto: @BayoOmoboriowo
Asali: Twitter

KU KARANTA: El-Rufai ya saki fursunoni 25, ya yi wa wasu rangwame

Gwamnan ya kuma koka kan yadda ambaliyar ruwa a bana ya lalata filaye masu yawa musamman gonakin rake a jihar.

Hakan yasa ya yi kira ga shugaban kasar ya taimakawa manoman jihar da ambaliyar ruwar ya sha kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito.

A wani labarin daban, wata kotu da ke Malmo a kasar Sweden ta yanke hukuncin cewa musulmi suna da ikon su rika tafiya suyi salla a lokacin da suke wurin aiki.

Hukuncin ya ce dole masu kamfanoni su rika barin ma'aikatansu Musulmi su rika yin sallolinsu biyar a lokacin da suke wurin aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel