An kai Shugaba Trump asibiti bayan kamuwa da korona

An kai Shugaba Trump asibiti bayan kamuwa da korona

- Shugaba Donald Trump na Amurka yanzu yana asibitin Walter Reed

- An garzaya da shugaban zuwa asibitin ne bayan ya kamu da cutar korona

- Shugabannin kasashe da dama sun aike masa da sakon fatan samun sauki

An tafi da Shugaba Donald Trump asibitin sojoji na Walter Reed. Hakan na zuwa ne bayan gwajin da aka yi wa shugaban na Amurka ya nuna ya kamu da cutar Covid 19 wato Coronavirus.

Asibitin sojojin yana wajen birnin Washington ne kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

An kai Shugaba Trump asibiti bayan kamuwa da korona
An kai Shugaba Trump asibiti bayan kamuwa da korona. Hoto: @CNN
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kotu ta bawa musulmi damar zuwa Sallah a lokutan aiki a Sweden

Idan za a iya tunawa Trump da mai dakinsa Melania sun kamu da korona a ranar Alhamis 2 ga watan Oktoba bayan wata hadimar shugaban, Hope Wicks ta kamu da cutar.

Kafin garzayawa da shi asibitin sojojin, an bawa shugaban na Amurka wasu magunguna.

Wannan bayanin na kunshe ne cikin wani sanarwa da likitan shugaban kasar ya fitar kamar yadda CNN ta ruwaito.

"A halin yanzu Shugaban kasa yana cikin yanayi mai kyau amma akwai gajiya tattare da shi. Wata tawagar kwararru na duba shi kuma tare da su zamu bada shawarar abinda ya dace a masa shi da mai dakinsa," a cewar likitan.

KU KARANTA: Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya

Shugabanin kasashen duniya da dama sun jajantawa Trump tare da masa fatan samun sauki da shi da mai dakinsa cikinsu har da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.

Rashin lafiyar na shugaba Donald Trump na zuwa ne a lokacin da kasar ta Amurka ke shirye-shiryen yin babban zaben ta a watan Nuwamba.

A wani rahoton daban, Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Alhamis ya sanar da sakin fursunoni 25, rage wa'adin wasu ciki har da waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa da aka sauya musu zuwa ɗaurin rai da rai.

Gwamnan ya sanar da hakan ne cikin jawabinsa na bikin ranar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴanci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel