Budurwar da ke yi wa saurayinta girki ta kai masa ta gano cewa tare da wata yake ci

Budurwar da ke yi wa saurayinta girki ta kai masa ta gano cewa tare da wata yake ci

- Wata mata mai suna Oluwafunlola ta wallafa a shafinta na Twitter yadda saurayinta ke cin abincin da ta girka tare da wata budurwarsa

- Duk lokacin da ta aika dan acaba da abincin, sai yayi karyar cewa dama ya aika da kudi a siyo masa ne a wani gidan abinci

- Duk da mutane da dama na ganin laifin maza akan rashin amana a soyayya, wasu kuma suna ganin laifin 'yanmatan da ke zakewa a soyayya

Wata budurwa mai suna Oluwafunlola, ta wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, yadda saurayinta ya yaudare ta.

Budurwar ta bada labarin yadda ta gano cewa saurayin da ta ke kauna yana da wata budurwa daban.

Ba wannan kadai ne yafi daga mata hankali ba, hankalinta ya tashi ne a lokacin da ta gano ashe amfaninta daya ne a wurin sa, wato girki.

Kuma ko girkin, ba shi kadai ne take yi wa ba, har da dayar budurwarsa.

A yadda budurwar ta bada labari, tana tura wa saurayin nata abinci ne ta masu babur din haya.

Idan dayar budurwar ta tambayi saurayin, sai ya ce ai dama aikawa yake yi ana siya mishi.

A yadda budurwar ta wallafa a shafinta na kafar sada zumunta: "A yau ne na gane cewa saurayin da nake wa girki cikin lokacin kullen nan, yaudara ta yake yi.

"Saboda tsananin soyayyar da nake mishi, dama yana rokona akan inyi mishi girki, sai in tura dan acaba da abincin. Ashe tare da wata budurwarsa suke ci. Yana yi mata karya ne, ya ce ya siyo abincin ne."

Wannan wallafar tata, ta jawo cece-kuce iri-iri a kafar sada zumuntar. Inda wasu ke yi mata Allah-ya- kara, wasu kuma suna tausaya mata.

KU KARANTA: 2023: Mun amince da shugabancinsa - Matasan arewa sun bayyana zabins

Budurwar da ke yi wa saurayinta girki ta kai masa ta gano cewa tare da wata yake ci
Budurwar da ke yi wa saurayinta girki ta kai masa ta gano cewa tare da wata yake ci. Hoto daga @Oluwafunlola
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga: Tubabben sarkin Zamfara ya maka IGP da wasu a kotu

A wani labari na daban, wata hira tsakanin budurwa da saurayi ta bazu a kafafen sada zumutar zamani wacce ta janyo tsokaci kala-kala daga jama'a, shafin Linda Ikeji ya wallafa hakan.

Kamar yadda hirar ta nuna, budurwar ta yi wa saurayin wankin babban bargo a kan kyautar da ya bata domin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta.

Kamar yadda hirar ta nuna, budurwa Tola ta caccaki saurayinta mai suna Babatunde, bayan da ya yi mata murnar zagayowar ranar haihuwarta kuma ya tura mata N15,000.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel