Kamuwa da Coronavirus: Buhari ya jajantawa Donald Trump kuma yayi masa addu'a

Kamuwa da Coronavirus: Buhari ya jajantawa Donald Trump kuma yayi masa addu'a

- Buhari ya bi sahun shugabannin kasashen duniya wajen jajantawa Trump da matarsa

- Trump ya killace kansa da iyalansa bayan kamuwa da cutar Korona

- Trump ya kamu ne bayan zuwa kamfe da daya daga cikin hadimansa

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika addu'o'insa ga shugaban kasan Amurka, Donal Trump, da uwargidarsa, Melania Trump, da suka kamu da cutar COVID-19.

Buhari ya aike sakonsa a jawabin da ya saki ranar Juma'a a shafinsa na Tuwita.

A cewarsa, kamuwa da cutar da Trump yayi ya nuna cewa irin hadarin da cutar ke da shi ga duniya gaba daya.

"Ina yiwa shugaban kasan Amurka, Donald Trump, da uwargidarsa, Melania, samun lafiya daga cutar COVID-19." Yace

DUBA NAN: Gwamnatin tarayya ta bada umurnin bude dukkan makarantu a Najeriya

Kamuwa da Coronavirus: Buhari ya jajantawa Donald Trump kuma yayi masa addu'a
Credit: @MBuhari
Source: Facebook

KU KARANTA: Kotu ta dakatar da KAROTA daga kama baburan adaidaita sahu marasa hatimi

Mun kawo muku rahoton cewa Shugaban kasar Amurka Donald Trump da matarsa Melania sun kamu da COVID 19 da aka fi sani da korona kimanin kwanaki 31 kafin zaben shugaban kasa na shekarar 2020 a kasar.

Shugaban kasar ya tabbatar da hakan a shafinsa na Twitter bayan daya daga cikin hadimansa Hope Hicks ya kamu da cutar tunda farko.

"A daren yau, ni da @FLOTUS mun kamu da COVID 19. Za mu killace kanmu ba tare da bata lokaci ba. Za mu ci gallaba a kan wannan tare!" kamar yadda ya rubuta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel