El-Rufai ya saki fursunoni 25, ya yi wa wasu rangwame

El-Rufai ya saki fursunoni 25, ya yi wa wasu rangwame

- Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya yi wa wasu fursunoni a jiharsa afuwa don bikin cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴanci

- El-Rufai ya saki fursunoni 25, ya rage wa wasu wa'addi sannan wasu da aka yanke wa hukuncin kisa an sauya musu zuwa ɗaurin rai da rai

- Gwamnan Plateau, Simon Lalong shima ya yi wa wasu fursunoni biyar afuwa ciki har da wanda aka yanke wa hukuncin kisa

Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a ranar Alhamis ya sanar da sakin fursunoni 25, rage wa'adin wasu ciki har da waɗanda aka yanke wa hukuncin kisa da aka sauya musu zuwa ɗaurin rai da rai.

Gwamnan ya sanar da hakan ne cikin jawabinsa na bikin ranar cikar Najeriya shekaru 60 da samun ƴanci.

El-Rufai ya saki fursunoni 25, ya yi wa wasu afuwa
El-Rufai ya saki fursunoni 25, ya yi wa wasu afuwa. Hoto: @GuardianNigeria/@daily_trust
Asali: Twitter

El-Rufai ya shawarci ƴan Najeriya su yi nazari kan shugabanci da yadda aka raba ayyuka da iko tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayya.

DUBA WANNAN: Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya

Ya ce, "A yayin da muke bikin cika shekaru 60 da samun ƴancin kai, al'adda ce yin afuwa ga wasu da ke gidan gyaran hali a jihar Kaduna.

"Don haka, za a saki fursunoni 25, wasu kuma an rage musu wa'adinsu ciki har da ƴan fashi da aka yanke wa hukuncin kisa da aka sauya musu zuwa ɗaurin rai dai rai."

A bangarensa, Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau a ranar Alhamis shima ya yi wa fursunoni biyar afuwa ciki har da wani Obinna John da aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

KU KARANTA: Ashariyar da wasu aku 5 ke yi wa mutane a gidan zoo yasa dole an raba su (Hotuna)

A cewar gwamnan John wadda ya riga ya yi shekaru 8 a gidan yari an masa rangwame daga hukuncin kisa zuwa shekaru 21 a gidan yari.

Sauran hudun kuma an musu afuwa baki ɗaya za a sake su su tafi gida.

A wani rahoton,Yan sanda a Enugu sun kama wani mutum da ya shiga wani wurin bauta ya kama abin bautar da ya ce ya hana mutanen garin cigaba, ya yi sanadin tabarbarewar kasuwanci tare da hana 'yan mata samun mazan aure.

Mutumin mai matsakaicin shekaru, Nnajiofor Donatus ya ce wahayi aka masa ya tafi ya cire abin bautar daga inda ya ke.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel