Sojoji sun kashe 'yan bindiga 312, sun ceto wadanda aka yi garkuwa da su 91
- Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe ƴan bindiga 312 sun kuma ceto mutum 91
- Kakakin Hedkwatar Tsaro, Manjo Janar John Enenche ne ya bada sanarwar a Abuja
- Enenche ya yi kira ga al'umma su cigaba da bawa rundunar gudunmawa da sahihan bayannan sirri
A cigaba da ƙoƙarin ta na dakile ta'addanci, Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe ƴan bindiga 312 ta kuma ceto mutum 91 da aka yi garkuwa da su a arewa maso gabashin kasar tsakanin watan Yuli zuwa Satumba.
Da ya ke yi wa ƴan jarida jawabi a Abuja, Kakakin Hedkwatar Tsaro, Manjo Janar John Enenche ya ce an kashe ƴan ta'adda da dama an kuma lalata maɓuyarsu ta harin sama, ƙasa da na ruwa.
DUBA WANNAN: Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya
Janar Enenche, yayin jawabin ya ce cikin watanni uku da suka gabata an kwato litar AGO 9,040,300 da ja DPK 33,500 yayin sumamen da soji suka kai.
Kakakin na hedkwatar tsaro ya ce sojojin sun kashe miyagu 1,708 da aka kama da aikata laifuka daban-daban aka kuma ƙwato bindigu da harsasai.
KU KARANTA: Ashariyar da wasu aku 5 ke yi wa mutane a gidan zoo yasa dole an raba su (Hotuna)
Ya yi kira ga al'umma su cigaba da bawa sojoji hadin kai ta hanyar basu sahihan bayannan sirri daga garuruwan su.
A wani labairn daban, Rundunar 'yan sandan jihar Delta na neman tsohon karamin ministan ilimi, Kenneth Gbagi ruwa a jallo kan zargin cin zarafin wasu ma'aikatansa a Signatious Hotel.
Tunda farko Legit.ng ta ruwaito cewa Gbagi wanda shine mai otel din, wai ya bada umurnin da tube ma'aikatansa hudu, uku mata da na miji daya a sannan aka dauki hotunansu da bidiyo aka baza a dandalin sada zumunta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng