Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya

Nigeria@60: Ɗan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durƙusa yana gaishe da mara lafiya

- Abdallah Muhammad, dan gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya yaba wa mahaifinsa kan ziyarar da ya kai

- Abdallah ya jinjina wa mahaifinsa bisa saukin kai da ya nuna na durkusawa har kasa ya gaishe da wasu marasa lafiyan

- Dan gwamnan ya ce mahaifinsa baya durkusa wa shugaban kasa, Sarki ko attajiri sai mutanensa kawai ya ke durkusawa

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed a ranar Alhamis 1 ga watan Oktoban 2020 ya ziyarci wasu asibitoci a jihar cikin bukukuwar murnar zagayowar ranar samun 'yancin Najeriya.

A yayin ziyarar gwaman ya biya wa wasu da ke asibitin kudaden magani da wasu abubuwa a asibititocin kamar yadda Linda Ikeji ta ruwaito.

Dan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durkusa wa mara lafiya a asibiti
Dan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durkusa wa mara lafiya a asibiti. Hoto: @Lindaikeji/Mrdulas
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Na kashe fiye da mutum 50 don sun kasa biyan kudin fansa - Shugaban masu garkuwa

Dan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durkusa wa mara lafiya a asibiti
Dan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durkusa wa mara lafiya a asibiti. Hoto: @Lindaikeji/Mrdulas
Source: Twitter

A ranar 1 ga watan Oktoban 2020 Najeriya ta cika shekaru 60 da samun 'yanci daga hannun turawan mulkin mallaka na Burtaniya.

Dan gwamnan, Abdullah Mohammed ya wallafa hoton gwamnan ya durkusa a kasa yana gaishe da wata mara lafiya da ke kan gado kuma ya yabawa kankan da kai irin na mahaifin nasa.

A cewar Abdullah, mahaifinsa baya durkusa wa Shugabannin kasa, Sarakuna, Attajirai sai dai talakawansa kawai.

KU KARANTA: 'Ka gayyato sojojin Chadi su taya mu yaki da Boko Haram' - Zulum ya roki Buhari

"Mahaifi na baya durkusa wa Shugaban kasa. Mahaifi na baya durkusa wa Sarki. Mahaifi na baya durkusa wa biloniya. Amma yana durkusa wa mutanensa #learninghumility," ya rubuta.

Dan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durkusa wa mara lafiya a asibiti
Dan gwamnan Bauchi ya wallafa hoton mahaifinsa ya durkusa wa mara lafiya a asibiti. Hoto: @Lindaikeji/Mrdulas
Source: Twitter

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, kun ji shugaban jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, na kasa Farfesa Tunde Adeniran a ranar Talata ya sanar da cewa ya yi murabus daga harkokin siyasa ta hammaya.

Adeniran ya sanar da hakan ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannunsa da kwanan watan 29 ga watan Satumban 2020 da ya aike wa hedkwatan jam'iyyar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel