Buhari ya tabbatar da tabarbarewar tattalin arziki da tsaro a Najeriya
- Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya sanar da cewa kasar nan tana cikin halin tabarbarewar tattalin arziki
- Ya kara da bayyana cewa, akwai manyan kalubale da kasar nan ke fuskanta na fannin tsaro a sassan kasar nan
- Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a yayin jawabi ga 'yan Najeriya a ranar cikar kasar shekaru 60 da samun 'yancin kai
A ranar Alhamis, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa kasar nan tana cikin mawuyacin hali a fannin tattalin arziki.
Ya ce hakan kuwa daidai yake da kowacce kasa domin kuwa dukkan duniya ne ake cikin wannan halin.
Buhari ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga 'yan Najeriya a ranar da kasar ta cika shekaru 60 da samun 'yancin kai.
Shugaban kasar ya kara da amincewa da cewa, kasar na fuskantar matsalolin tsaro daban-daban a sassan kasar.
Ya ce, "A yau na tabbatar da cewa Najeriya tana cikin mawuyacin hali na tattalin azriki kuma hakan ce ta kasance ga kowacce kasa a fadin duniya. Muna fuskantar kalubalen tsaro a sassa daban-daban na kasar nan."
KU KARANTA: Mutum na farko da ya warke daga cutar HIV ya rasu sakamakon cutar Cancer

Asali: Twitter
KU KARANTA: Fyade: Kotu ta kori soja daga aiki, ta yanke masa hukuncin shekaru 5 a gidan yari
A wani labari na daban, kungiyar Igbo for President Solidarity Congress (IPSC), wata kungiya ce a kudu maso yammacin Najeriya, ta tabbatar da bada hadin kai dari bisa dari akan shugabancin dan kudu maso gabas a shekarar 2023.
Ta ce yin hakan ne kadai zai kawo hadin kai a Najeriya. Shugaban kungiyar, Dr Olukayode OshinAriyo ne yayi wannan kiran a ranar Talata, 29 ga watan Satumba a Ibadan, jihar Oyo.
IPSC ta ce kamar yadda kundin tsarin mulkin 1999 ya nuna, kudu maso gabas suna da damar rike kujerar shugabancin kasar Najeriya.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng