Da duminsa: Shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa ya yi murabus daga harkokin siyasa

Da duminsa: Shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa ya yi murabus daga harkokin siyasa

- Shugaban jam'iyyar SDP na kasa, Farfesa Tunde Adeniran ya sauka daga mukaminsa ya kuma yi murabus daga siyasar hammaya

- Farfesa Adeniran ya ce ya yi shawara da masu ruwa da tsaki na jam'iyyar da wasu magoya bayansa kafin daukan matakin

- A cewarsa, lokaci ya yi da zai koma gefe ya zama dattijo yana bada shawarwari saboda haka murabus dinsa baya nufin zai dena bada gudunmawarsa wurin cigaba a kasar

Da duminsa: Shugaban SDP na kasa ya yi murabus daga siyasa
Da duminsa: Shugaban SDP na kasa ya yi murabus daga siyasa. Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun afka wa mutane a Wasagu, sun kashe guda sun raunata da dama

Shugaban jam'iyyar Social Democratic Party, SDP, na kasa Farfesa Tunde Adeniran a ranar Talata ya sanar da cewa ya yi murabus daga harkokin siyasa ta hammaya.

Adeniran ya sanar da hakan ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannunsa da kwanan watan 29 ga watan Satumban 2020 da ya aike wa hedkwatan jam'iyyar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Ya ce, "Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jam'iyyar da wasu masu goyon baya na da ke fatan ganin cigaban jam'iyyar, ina son sanar da jama'a cewa na yi murabus daga siyasa.

KU KARANTA: An sace shugaban karamar hukuma a hanyarsa ta zuwa gona a Kaduna

"Hakan na nufin zan sauka daga mukamin da na ke rike da shi yanzu kuma ba zan sake shiga harkokin siyasa ta hammaya ba."

Adeniran ya yi bayanin cewa ya san babban kallubalen da ke gaban yan siyasa a wannan zamanin amma ya kai matsayin da zai fi yi wa kasar amfani a matsayin dattijo.

"Akwai bukatar dukkan masu kishin kasa su mayar da hankali domin cimma abinda suka saka a gaba. Murabus di na baya nufin zan cire hannu na daga siyasan kasar mu amma siyasar hammaya ne zan dena," in ji shi.

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata 29 ga watan Satumban ya kaddamar da aikin layin dogo na takpe-Ajaokuta-Agbor-Warri ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo mai nuna bidiyo da sauti.

An yi bikin ne a tashan jirgin kasa na Agbo inda aka saka wa tashar sunan tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan. Read more:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel