Hotunan fitattun mata 3 da suka jajirce wurin ganin samun 'yancin Najeriya

Hotunan fitattun mata 3 da suka jajirce wurin ganin samun 'yancin Najeriya

- Mata 3 da suka jajirce wurin taimakawa har Najeriya ta samu 'yancin kanta

- Matan nan sun nuna jarumta a harkar siyasa da kirkire-kirkiren jam'iyyu a Najeriya

- Sun dage har sai da Turawa suka ba Najeriya 'yancin kanta a shekarar 1960

Yayin da 'yan Najeriya ke shirye-shiryen fara bikin murnar cikar Najeriya shekaru 60 da samun 'yancin kai a 1 ga watan Oktoba, zai kyautu a tuna mata 3 da suka taka babbar rawa wurin cigaban ganin hakan.

Ba matan nan 3 ne kadai suka kawo duk cigaban kasar nan ba, sai dai a wannan rubutun, zamu fi bada muhimmanci akan su.

Fitattun mata 3 da suka jajirce wurin ganin samun 'yancin Najeriya
Fitattun mata 3 da suka jajirce wurin ganin samun 'yancin Najeriya. Hoto daga Independent
Asali: UGC

Mata 3 da suka taka babbar rawa kafin da bayan Najeriya ta samu 'yancin kanta.

KU KARANTA: Rundunar soji sun halaka 'yan bindiga 2, sun cafke 3 a Kaduna - DHQ

1. Funmilayo Ransome-Kuti

Ita ce matar da aka sa wa suna 'Zakanyar Lisabi'. Babbar malama ce, wadda ta kirkiri kungiyar matan Najeriya a 1953, kuma ta jajirce akan kare hakkin mata kafin Najeriya ta samu 'yancin kanta.

Kuti tana daya daga cikin matan Najeriya da suka kirkiri jam'iyyun siyasa. Sai da rayuwarta ta zama madubin dubawar matan Najeriya da dama.

Tana daya daga cikin jiga-jigan da suka amsar wa Najeriya 'yancin kanta daga hannun Turawa. An haife ta 25 ga watan Oktoba 1900, kuma ta rasu ranar 13 ga watan Afirilu 1978.

Fitattun mata 3 da suka jajirce wurin ganin samun 'yancin Najeriya
Fitattun mata 3 da suka jajirce wurin ganin samun 'yancin Najeriya. Hoto daga Litcaf
Asali: UGC

2. Hajiya Gambo Sawaba.

An haifeta a 15 ga watan Fabrairu, 1933. Mahaifinta dan kasar Ghana ne, mahaifiyar ta kuma banufiya ce. Ta fara harkar siyasa tun tana da shekaru 17 a duniya.

Sakamakon auren wuri da aka yi mata, tayi amfani da jamiyyar Northern Elements Progressive Union (NEPU), wurin jajirce wa akan hana auren wuri a Najeriya.

Hajiya Sawaba ta kuma tsaya tsayin-daka wurin hana auren dole da kuma dagewa akan ilimin boko.

Fitattun mata 3 da suka jajirce wurin ganin samun 'yancin Najeriya
Fitattun mata 3 da suka jajirce wurin ganin samun 'yancin Najeriya. Hoto daga Nigeria Galleria
Asali: UGC

KU KARANTA: Nufin Allah: Dattijuwa ta zama cikakkiyar likita tana da shekaru 50 (Hotuna)

3. Margaret Ekpo

An haife ta a shekarar 1914. Ta kirkiri Kungiyar matan Aba a shekarar 1954, a kuma wannan shekarar NCNC ta zabe ta a matsayin yar majalisar Dattawa.

Sannan an kara zaben ta a matsayin 'yar majalisar yankin gabas a shekarar 1961 da 1965. Ta rasu ranar 21 ga watan Satumba, 2006.

Fitattun mata 3 da suka jajirce wurin ganin samun 'yancin Najeriya
Fitattun mata 3 da suka jajirce wurin ganin samun 'yancin Najeriya. Hoto daga Independent
Asali: UGC

A wani labari na daban, Kabilar Kanuri sananniyar kabila ce a kasarnan. A yadda tarihi ya nuna, kanuri itace sananniyar kabila a jihar Borno ta samu asali ne daga Yemen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel