Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin dindindin hudu (Sunaye da jihohi)

Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin dindindin hudu (Sunaye da jihohi)

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana jagorantar taron Majalisar Zartarwa na Kasa, FEC, a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja

- Gabanin fara taron, Shugaba Buhari ya rantsar da sakatarorin dindindin guda hudu maza uku da mace guda daya

- Wadanda aka nada sune James Sule, Ismaila Abubakar, Ibiene Patricia Roberts da Shehu Aliyu Shinkafi

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya rantsar da sabbin sakatarorin dindindin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

An yi takaitaccen bikin rantsar da sakatarorin ne kafin fara taron Majalisar Zartarwa na Tarayya, FEC, da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo mai nuna bidiyo da sauti.

Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin dindindin hudu (Sunaye da jihohi)
Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin dindindin hudu (Sunaye da jihohi). Hoto: @Buharsallau1
Source: Twitter

Sakatarorin da aka rantsar a gidan gwamnatin sune James Sule daga Jihar Kaduna, Ismaila Abubakar daga Jihar Kebbi, Ibiene Patricia Roberts daga jihar Rivers da Shehu Aliyu Shinkafi daga jihar Zamfara.

DUBA WANNAN: Fusatattun matasa sun kai wa hadimin gwamnan Jigawa hari

Sabbin sakatarorin hudu da aka rantsar da suka hada da maza biyu da mace daya cikon wasu 12 ne da aka rantsar kimanin wata daya da ta gabata yanzun sun cika 16.

A halin yanzu shugaban kasar yana jagorantar taron FEC a fadarsa da ke Abuja. Wadanda suka samu halarta sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari, NSA Babagana Monguno da ministoci hudu.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun afka wa mutane a Wasagu, sun kashe guda sun raunata da dama

Ministocin sune Ministan shari'a, Abubakar Malami; Ministan Kudi, Kasafi da Tsarin Kasa, Zainab Ahmed; Ministan Sadarwa da Al'adu, Lai Mohammed sai Karamin ministan Kasafi da Tsarin kasa, Clement Agba.

Sauran mambobin majalisar suna hallartar taron daga ofisoshinsu ta fasahar yanar gizo mai nuna bidiyo da sauti.

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata 29 ga watan Satumban ya kaddamar da aikin layin dogo na takpe-Ajaokuta-Agbor-Warri ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo mai nuna bidiyo da sauti.

An yi bikin ne a tashan jirgin kasa na Agbo inda aka saka wa tashar sunan tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel