Damfara: Shugaban KAROTA zai gurfana a gaban kotu

Damfara: Shugaban KAROTA zai gurfana a gaban kotu

- A ranar Laraba , 30 ga watan Satumba ne shugaban hukumar KAROTA na jihar Kano zai bayyana a gaban kotu

- Wasu 'yan adaidaita sahu ne suka maka shugaban hukumar a gaban kuliya bayan zarginsa da suke da zamba cikin aminci

- Sun ce shugaban ya karbe musu makuden kudadensu a kan wata na'ura amma har yanzu shiru kake ji

A yau Laraba ne ake sa ran shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan-Agundi, zai bayyana a gaban wata kotun majistare da ke jihar Kano a kan zarginsa da ake da zamba cikin amici da yaudara.

Kamar yadda kotun ta bada umarni, kotun na bukatar ganin shugaban KAROTA da kan sa ba wakili ba saboda girman laifin da ake zarginsa., Freedom Radio ta wallafa.

A karkashin mai shari’a Muhammad Jibril, kotun ta gayyaci Baffa Babba bayan kararsa da wasu direbobin adaidaita sahu suka shigar a gaban kotun.

Sun ce an yaudaresu a kan wata na’ura kuma an karbe musu kudade da sunan za a basu.

Barista Abba Hikima, babban lauya a jihar Kano, shi ke wakiltar masu gabatar da karar kuma ya bayyana a gaban kotun.

KU KARANTA: Matashin da ya kashe iyayensa, matarsa da kanwar matarsa ya mika kansa ga 'yan sanda (Hotuna)

Damfara: Shugaban KAROTA zai gurfana a gaban kotu
Damfara: Shugaban KAROTA zai gurfana a gaban kotu. Hoto daga Triumph
Source: Facebook

KU KARANTA: Rundunar soji sun halaka 'yan bindiga 2, sun cafke 3 a Kaduna - DHQ

A wani labari na daban, Wahab Shitu, lauya mai kare shugaban EFCC, Ibrahim magu, ya ce wanda yake karewa bai amsa laifin da ake zarginsa ba.

A wata magana ta daban, an yadda cewa Magu ya ce da kwamitin binciken ya firgita a matsayinsa na shugaban EFCC kuma ya nemi yafiya.

Kamar yadda lauyan ya ce, tsohon shugaban EFCC bai amince da rashawar da ake zarginsa dashi ba, kuma bai roki gafarar kowa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel